Dalilinmu na yin taro da Obasanjo, Afenifere da sauransu - Dattawan arewa

Dalilinmu na yin taro da Obasanjo, Afenifere da sauransu - Dattawan arewa

- A daren Lahadi, kungiyar dattawan arewa ta sanar da dalilinta na yi taron tsawon kwanaki biyu da Obasanjo tare da waus kungiyoyi a kasar nan

- Wata majiya wacce ta bukaci a boye sunanta ta sanar da cewa, gwamnoni uku sun samu halartar gagarumin taron tattaunawa

- Kamar yadda Dr. Hakeem Baba-Ahmed ya bayyana, sun tattauna a kan manyan matsalolin da ke wa kasar nan barazana

Kungiyar dattawan arewa a ranar Lahadi da dare ta bayyana dalilinta na tattaunawa da tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo tare da kungiyar Afenifere.

Dr. Hakeem Baba-Ahmed, ya ce sun tattauna da su domin shawo kan matsaloli da manyan kalubale da ke addabar kasar nan, Daily Trust ta wallafa.

An yi taron da Obasanjo, shugabannin kungiyar Afenifere, dattawan arewa, ohaneze Ndigbo da wata kungiyar 'yan yankin Neja Delta, sun yi taron tattaunawa na tsawon kwanaki biyu a Abuja.

A wannan taron ne Obasanjo ya sanar da matsayarsa na cewa kasar nan na daidaicewa tare da lalacewa karkashin mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Duk da an yi taron a sirrance, takardar tsohon shugaban kasa Obasanjo ta fita bayan taron.

Wata majiya daga wurin tattaunawar, ta ce akwai gwamnoni uku da suka halarci taron. Sun hada da shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, Gwamna Kayode Fayemi na jihar Ekiti, Atiku Bagudu na jihar Kebbi da Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto.

"Ba taron sirri bane kamar yadda ake sanarwa ko hasashe. Mun hada kuma mun fitar da abubuwan da muka tattauna," majiyar ta sanar amma ta bukaci a boye sunanta.

Majiyar ta ce tsohon shugaban kasa Obasanjo ya tuntubi shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, kafin a yi tattunawar.

KU KARANTA: Hotunan cikin katafaren gidan Rihanna na London wanda za a siyar a 14 biliyan

Dalilinmu na ziyartae Obasanjo, Afenifere da sauransu - Dattawan arewa

Dalilinmu na ziyartae Obasanjo, Afenifere da sauransu - Dattawan arewa. Hoto daga Daily Trust
Source: Twitter

KU KARANTA: 'Yan sanda sun cafke makusancin Gwamna Yari yana taron sirri da 'yan bindiga a Zamfara

"Gambari ya dauka alkawarin sanar da shugaban kasa a kan abinda ya faru. A taron, Fayemi ya dauka alkawarin sanar da shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan abinda aka tattauna," majiyar tace.

A wata tattaunawa ta waya da aka yi, Baba-Ahmed ya jajanta yadda 'yan Najeriya suka mayar da hankali a kan maganar Obasanjo a maimakon matsalolin da suka tattauna a taron.

"Kamar yadda yace, abubuwa da dama sun faru. Akwai abubuwa da yawa da muka tattauna a kan halin da kasar nan ke ciki.

"Kowacce kungiya ta bayyana matsayarta da kuma matsalolin da take fuskanta a kasar nan. Kuma mun mayar da hankali wurin ganin mun shawo kan wannan kalubalen.

"Muna da matsaloli da juna, muna da matsala ta baya amma mun aminta da cewa za mu bankado su tare da gyara su. Taron ya kare cike da tunanin ganin sauyi," cewar Baba-Ahmed.

A wani labari na daban, wani babban jami'i a fadar shugaban kasa ya gaggauta yi wa tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, martani a kan ikirarinsa na daidaicewar Najeriya karkashin mulkin shugaban kasa Buhari.

Duk da babban mai bai wa shugaban kasar shawara na musamman a fannin yada labarai, Garba Shehu, bai yi martani ba, babban jami'in wanda bai bukaci a bayyana sunansa ba, ya kwatanta Obasanjo da mutumin da.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel