Farfesa Jega, Bugaje, Agwai, Balla sun ba Buhari shawarar gyara kasar nan
- Wata Kungiya ta fito ta fadawa Gwamnati sirrin kawo zaman lafiya
- Kungiyar ta ce dole a kawo karshen rashin tsaro da ake fama da shi
- ‘Yan kungiyar sun hada da Attahiru Jega, Usman Bugaje da Onaiyekan
Hanyar da za a bi a iya kawo karshen matsalolin da Najeriya ta ke fama da su shi ne a fara zama a tattauna yadda za a ga an wanzar da zaman lafiya.
Wata kungiya mai dauke da fitattun manya da masana a Najeriya, sun nemi shugaban kasa Buhari da gwamnonin jihohi su shirya zaman tattaunawa.
Wannan kungiya ta ce da zaman sulhu ne za a cin ma kalubalen da ake fama da su na rashin tsaro. Daily Trust ta fitar da wannan rahoto a ranar Lahadi.
Kungiyar ta ce al’ummar kasa su na cikin wani mawuyacin hali a sakamakon rashin tsaro da annobar cutar COVID-19 da su ka yi wa ‘yan kasar zobe.
KU KARANTA: Jonathan ya bayyana abin da zai yi maganin magudin zabe
Wadanda su ka sa hannu a takardar da wannan kungiya ta fitar su ne: Cardinal John Onaiyekan, Janar Martin Luther Agwai (mai ritaya), Farfesa Attahiru Jega.
Saura sun hada da: Ambasada Fatima Balla, Farfesa Jibrin Ibrahim, Aisha Mohammed-Oyebode, Dr. Nguyan Shaku Feese, Dr. Usman Bugaje da Dr. Chris Kwaja.
A cewar kungiyar, har yanzu ana fama da matsalar rashin tsaro, don haka ta fito ta yi magana a lokacin da Olusegun Obasanjo ya ke kokawa da halin da ake ciki
Wadannan gawurtattun masana da shugabanni sun ce yanzu ne lokacin da za a shawo kan matsalar rikicin addini da kabilanci, da kuma yaki da COVID-19.
KU KARANTA: Buhari: Malaman addini sun fara fitowa su na kukan tsadar rayuwa
Jega da sauran abokansa su ka ce gwamnati za ta bata lokaci a banza idan aka kawo karshen annobar Coronavirus ba tare da an yi maganin matsalar rashin tsaro ba.
Haka zalika, kungiyar ta ce ‘yan kasa su na da rawar da za su taka wajen samar da zaman lafiya, musamman a yanzu da ake ganin jami’an tsaro sun gaza.
A cewar kungiyar, dole gwamnati ta shirya zaman sulhu da tattaunawa da al’umma a kowane bangare, idan har ana da niyyar ganin an samu kwanciyar hankali.
Wannan kungiya ta bada shawarar maye gurbin shugabannin jami’an tsaro da hafsun soji, ta ce akwai bukatar a kai ga tsigesu idan hakan zai inganta sha’anin tsaro.
A baya an samu kungiyar ta yi akasin irin wannan kira na sauke hafsun sojojin kasa.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng