Rikicin NBA: Lauyoyi sun huro wuta a cirewa Minista mukamin ‘SAN’
- An taso Ministan shari’a a gaba, har ana kiran a tsige shi daga SAN
- Ana korafin cewa Abubakar Malami ya ci amanar ofishinsa na AGF
- Lauyoyi fiye da 300 sun sa hannu a raba Ministan da mukamin SAN
Lauyoyi sama da 300 a Najeriya su ke neman a tsigewa ministan shari’an Najeriya, Malam Abubakar Malami, mukaminsa na babban Lauya watau SAN.
Jaridar Punch ta ce wadannan lauyoyi sun bukaci a cirewa babban lauyan gwamnatin tarayya mukaminsa na SAN ne a dalilin yunkurin ragewa NBA karfi.
Wani Bawan Allah Izu Aniagu, shi ne ya kirkiro wannan korafi a shafin yanar gizo, inda ya ke kira ga sauran mutane su taya shi kiran a cirewa ministan mukaminsa.
Mista Izu Aniagu ya yi wa wannan korafi taken ‘Sa hannu a cirewa babban lauyan gwamnatin tarayya, AGF, Abubakar Malami, mukamin babban lauyan Najeriya.”
KU KARANTA: Kungiya ta nemi Buhari ya binciki Malami SAN
Aniagu ya shigar da wannan korafi ne a shafin change.org a cikin karshen makon da ya gabata.
Lauyoyi akalla 380 a Najeriya su ka sa hannu a wannan korafi kamar yadda jaridar Punch ta fitar da rahoto a yammacin ranar Lahadi, 13 ga watan Satumba, 2020.
Hakan na zuwa ne bayan Ministan ya yi wasu garambawul a dokokin shari’a na shekarar 2007, inda ya taba wasu daga cikin ikon da aka ba kungiyar Lauyoyi ta NBA.
Izu Aniagu ya ce kwaskwarimar da AGF ya ke yi wa dokokin kasa su na da hadari, sannan ya ce Abubakar Malami SAN ya kan sabawa dokokin kotu da dokarsa.
KU KARANTA: A fito da Zakzaky tun da an saki Dasuki - Falana
Har ila yau, Izu Aniagu, ya zargi Ministan da kin binciken wasu da ake zargi da laifi. A cewar Aniagu, Malami ya kan kare wasu marasa gaskiya da ke kusa da shi.
A dalilin wannan abu da ya kira son kai, Aniagu ya yi kira ga mutane su sa hannu a wannan korafi da ke neman a raba Malami da mukaminsa na babban Lauya, SAN.
Zuwa karfe 8: 00 na ranar Lahadi, Lauyoyi 383 sun sa hannu a wannan korafi inji jaridar.
A baya kun ji cewa an samu rabuwar kai bayan NBA ta janye gayyatar da ta aikawa gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai wajen babban taron da ta shirya na shekarar nan.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng