Wani mutum ya kashe gwaggonsa mai shekaru 60 da hannunsa

Wani mutum ya kashe gwaggonsa mai shekaru 60 da hannunsa

- Wani matashi mai shekaru 23 ya kashe gwaggonsa da hannunsa

- An gano hakan ne bayan matashin ya fallasa kansa sakamakon barazana da wani mai magani yayi na aika fatalwan marigayar domin farautar makashinta

- Rundunar yan sandan jihar Ogun ta tabbatar da afkuwar lamarin, ta ce ta kama matashin kuma tana bincikensa

Wani matashi mai shekaru 23 a yankin Ipokia da ke jihar Ogun, Dansu Asogba, ya tonawa kanshi asiri bayan ya kashe gwaggonsa mai shekaru 60, Iyabo Dansu.

Ya fallasa kansa ne bayan wani mai magani ya yi barazanar tura fatalwan marigayiyar domin yin farautan makashinta.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya bayyana hakan a cikin wani jawabi a ranar Lahadi, jaridar Punch ta ruwaito.

Oyeyemi ya yi bayanin cewa an kama wanda ake zargin bayan ya fallasa ta’asar da ya aikata.

KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun sace yan gida daya su 17 a Kaduna

Wani mutum ya kashe gwaggonsa mai shekaru 60 da hannunsa

Wani mutum ya kashe gwaggonsa mai shekaru 60 da hannunsa Hoto: Premium Times
Source: Depositphotos

A cewarsa, an damke wanda ke zargin ne bayan wani rahoto da yaran marigayiyar biyu suka kai hedkwatar rundunar da ke Ipokia.

Ya ce: “Sun kai karar cewa sun samu bayanai a ranar 22 ga watan Agusta, 2020 game da mutuwar mahaifiyarsu wacce bata yi fama da kowani rashin lafiya ba.

“Sun bayyana cewa tunda basu zargi komai ba, sai suka yanke shawarar binne ta ba tare da sun sanar da yan sanda ba.

“Amma bayan binne ta, sai suka samu labarin cewa an gano wanda ake zargin, wanda ya kasance dan uwan marigayiyar, a gidanta a wannan rana, sannan jim kadan bayan wucewarsa, sai aka samu matar ta mutu.

“Hakan ya sa suka fara zargin wani abu sannan suka yi barazanar dauko mai maganin gargaiya wanda zai fallasa wanda ya kashe ta. Da ya ji labarin kudirin jama’ar gari a kan marigayiyar, sai wanda ake zargin Dansu Asogba ya fito ya fallasa kansa cewa shine ya kashe ta.”

Oyeyemi ya ce bayan ya fallasa kansa, sai DPO na rundunar yan sandan Ipokia, SP Adebayo Hakeem ya tura jami’an yan sanda zuwa wajen, sannan suka kamo shi.

Da aka yi masa tambayoyi, wanda ake zargin ya yarda cewa shine ya kashe marigayiyar, inda ya yi ikirarin cewa ya aikata hakan ne saboda ya yarda cewa ita ta kashe masa dansa na fari da kuma bari da matarsa tayi.

KU KARANTA KUMA: Matar Alaafin Aishat ta ce mijinta ya fi matasa da dama iya tarairayan mace

Oyeyemi ya kara da cewa: “ya tona cewa ya yi amfani da rodi ne ya daki matar a wuya wanda ya yi sanadiyar mutuwarta.

“A halin da ake ciki, kwamishinan yan sandan jihar, Edward Ajogun, ya yi umurnin mayar da mai laifin zuwa sashin binciken masu manyan laifi domin ci gaba da bincike.”

A wani labari na daban, mun ji cewa yan sanda sun kama fitaccen dan fashi da makami kuma mai garkuwa da mutane, Honest Diigbara, wanda aka fi sani da Boboski.

Amma kuma kamun nashi bai zo da sauki ba, saboda sai da jami'an tsaro da 'yan sintiri a Korokoro da ke karamar hukumar Tai suka yi musayar wuta da shi.

Boboski ya mutu a yayin da yake hedkwatar 'yan sanda ta Fatakwal, tare da dan uwansa wanda shine direbansa kuma ya mutu a take bayan kamasu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel