Tsawa ta kashe dattawa uku a jihar Katsina

Tsawa ta kashe dattawa uku a jihar Katsina

- Tsawa ta kashe magidanta uku a kauyen Kukar-Gesa da ke karamar hukumar Katsina ta jihar Katsina

- Kamar yadda iyalan mamatan suka sanar da Vanguard, mazan uku sun rasu ne sakamakon tsawa da aka yi yayin da ake ruwan sama

- Manoman biyar ne suka fake a kasan wata bishiya a gonarsu, amma sai uku suka rasu yayin da biyu suka raunata

Tsawa ta kashe mutum hudu cikin manoma biyar da suka fake a kasan bishiya yayin da ake tafka mamakon ruwan sama a kauyen Kukar-Gesa da ka karamar Katsina ta jihar Katsina.

Malam Musa Danladi, shugaban iyalan ya tabbatar da mutuwar 'ya'yansa biyu da jikansa daya kuma ya danganta hakan da hukuncin Ubangiji.

"Ruwan ya fara wurin karfe 5 na yamma a ranar Asabar, yayin da manoma biyar daga gidanmu suka je girbe geron daga gona," yace.

Majiya daga iyalan ta sanar da Vanguard a ranar Lahadi cewa, a lokacin da tsawar ta fada a kan bishiyar, uku daga cikin manoman sun rasa rayukansu yayin da biyun suka samu miyagun raunika.

Iyalan sun sanar da mutuwar mutum ukun bayan tsayawar ruwan saman wurin karfe 11 na dare kuma har lokacin ba a gansu ba.

Iyalan sun tura wasu jama'a don su binciko inda gawawwakin suke kuma su ceto sauran, lamarin da suka yi nasara sannan suka mika masu raunin asbiti.

An birne mamatan uku a safiyar Lahadi a makabartar kauyen Kukar-Gesa kamar yadda addinin Islama ya tanadar.

KU KARANTA: 2023: An kaddamar da yakin neman zaben shugabancin kasa na Tinubu

Tsawa ta kashe dattawa uku a jihar Katsina

Tsawa ta kashe dattawa uku a jihar Katsina. Hoto daga Vanguard
Source: Getty Images

KU KARANTA: Yadda kasurgumin mai garkuwa da mutane, Bobiski, ya mutu a hannun 'yan sanda

A wani labari na daban, akalla mutane 16 sun rasa rayukansu yayinda gidaje 2,000 suka salwanta sakamakon annobar ambaliyar ruwan sama a jihar Bauchi a shekarar 2020.

A rahoton da Jaridar Punch ta yi, an yi ambaliya a kananan hukumomin jihar da dama. Hukumar agajin gaggawa ta jihar Bauchi ta tabbatar da hakan a hirarta da Punch ranar Juma'a.

Sakataren din-din-din hukumar SEMA, Habu Ningi, ya ce ambaliyar ta shafi garuruwa 11 a kananan hukumomi fiye da goma.

Yace, "Mun ziyarci dukkan wuraren da ambaliyar bana ta shafa. Kawo yanzu mun samu rahotanni 11 a kananan hukumomi 11 na jihar.

"Zuwa yanzu, mutane 16 sun rasa rayukansu, 11 a karamar hukumar Bauchi, 1 a karamar hukumar Warji, 2 a karamar hukumar Shira, 2 a karamar hukumar Dambam."

"Sama da gidaje 2,000 sun ruguje sakamakon ambaliyar. An asarar amfani gona a gonaki 1,117."

"Gwamnatin jihar ta taimakawa mutanen da wannan abu ya shafa da kayayyaki domin rage radadin annobar."

Ningi ya shawarci mazauna su daina gina gidaje a magudanar ruwa kuma su daina zuba shara a cikin rafuka.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel