Hukuncin kisa a kan mawaki: Falana ya maka FG da gwamnatin Kano a gaban kotu

Hukuncin kisa a kan mawaki: Falana ya maka FG da gwamnatin Kano a gaban kotu

- Lauya mai rajin kare hakkin dan Adam, Femi Falana ya mika korafi a kan hukuncin kisa da aka yanke wa matashi a Kano

- Lauyan ya mika korafin gaban hukumar kare hakkin dan Adam da ke Banjul, a kasar The Gambia

- Ya yi kira ga hukumar da ta tsaya tsayin daka tare da karfin isarta domin tabbatar da cewa hukuncin bai yi aiki ba

Lauya mai rajin kare hakkin dan Adam kuma babban lauyan Najeriya, Femi Falana, ya mika korafi ga hukumar kare hakkin dan Adam da ke Banjul, kasar Gambia, a kan hukuncin kisa da aka yanke wa mawakin Kano.

Falana ya bukaci hukumar da ta yi amfani da karfin isarta kamar yadda dokokin hukumar ta bayyana na 2020.

Falana a korafinsa mai kwanan wata 8 ga Satumban 2020, ya ce: "Ina korafi a madadin Sharif Yahya Sharif inda nake bukatar hukumar da ta duba matakanta.

"Wannan bukatar mun miko ta a madadin Sharif Yahya Sahif wanda aka yanke wa hukuncin kisa ta hanyar rataya sakamkaon batanci da yayi a jihar Kano da ke Najeriya."

KU KARANTA: Da duminsa: An garkame zauren majalisar Ondo, an hana 'yan majalisar shiga

Hukuncin kisa a kan mawaki: Falana ya maka FG da gwamnatin Kano a gaban kotu

Hukuncin kisa a kan mawaki: Falana ya maka FG da gwamnatin Kano a gaban kotu. Hotp daga Vanguard
Source: Twitter

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Makarantar horon hafsoshin 'yan sanda ta saka ranar jarabawar shiga

Idan za mu tuna Legit.ng ta ruwaito cewa, majalisar limaman masallatan Juma'a na jihar Kano, sun jinjinawa hukuncin da aka yanke wa matashin da ya yi batanci ga Annabi Muhammad.

An yankewa matashi Yahaya Sharif-Aminu hukuncin kisa ne a wata kotu da ke jihar Kano a kan wakar batanci da ya yi ga Annabi Muhammad S.A.W.

Shugaban majalisar, Muhammad Nasir Adam, kamar yadda Kano Focus ta ruwaito, ya yi kira ga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar da ya sa hannu a kan takardar.

Gwamnan har yanzu bai yi martani a kan hukuncin ba.

Sharif-Aminu, mazaunin kwatas din Sharifai da ke birnin Kano, an maka shi gaban kotu ne sakamakon batanci da ya yi ga Annabi, wanda hakan ya ci karo da sashi na 382, sakin layi na 6 na dokokin shari'ar Musulunci na jihar Kano.

Mawakgin ya yi kalaman batancin ne cikin waka wacce ya watsa ta a kafar sada zumuntar zamani ta WhatsApp a watan Maris na 2020.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel