Daidaicewar Najeriya: Buhari da ACF sun yi wa Obasanjo martani mai zafi

Daidaicewar Najeriya: Buhari da ACF sun yi wa Obasanjo martani mai zafi

- Babban jami'i a fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya yi wa Olusegun Obsanjo martani

- Ya kwatantasa da mutumin da kuma tsoho bai san abinda ke faruwa a yanzu ba, amma sai iya kalubale maras tushe

- Shugaban ACF, Audu Ogbeh ya ce tsoffin shugabannin kasa kamar Gowon, Abdulsalami da Babangida duk suna kama mutuncinsu

Wani babban jami'i a fadar shugaban kasa ya gaggauta yi wa tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, martani a kan ikirarinsa na daidaicewar Najeriya karkashin mulkin shugaban kasa Buhari.

Duk da babban mai bai wa shugaban kasar shawarana musamman a fannin yada labarai, Garba Shehu, bai yi martani ba, babban jami'in wanda bai bukaci a bayyana sunansa ba, ya kwatanta Obasanjo da mutumin da.

Ya ce: "Obasanjo mutumin da ne. Ya yi suka ga shugaba Buhari kuma ya ci zabe, ba za a taba tsammanin cewa zai taba yabonsa ba."

Obasanjo a ranar Alhamis ya ce a hankali Najeriya take tabarbarewa tare da daidaicewa a karkashin mulkin Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Daily Trust ta wallafa.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Makarantar horon hafsoshin 'yan sanda ta saka ranar jarabawar shiga

Daidaicewar Najeriya: Buhari da ACF sun yi wa Obasanjo martani mai zafi

Daidaicewar Najeriya: Buhari da ACF sun yi wa Obasanjo martani mai zafi. Hoto daga Daily Trust
Source: Twitter

KU KARANTA: Bidiyo: Ina son kasancewa da shi har abada - Mahaifiya mai soyayya da danta

A yayin martani ga tsokacin Obasanjo, shugaban kungiyar 'yan arewa kuma tsohon ministan noma, Audu Ogbeh, a wata tattaunawa da yayi da Daily Trust a ranar Lahadi, ya ce wannan rashin dattako ne.

Ya ce: "Bayyana tabarbarewar Najeriya rashin dattako ne. Bari in sanar da wani abu, yana da nashi kalubalen a tattare da shi. Ina Zaki Biam da Odi? Babu wanda yace maka ka isa ka duba yadda wasu shugabanni ke aiki."

A yayin tunatar da Obasanjo, Ogbeh wanda tsohon shugaban jam'iyyar PDP ne zamanin mulkin Obsanjo, ya ce: "Ina tunanin idan da Gowon, Abdulsalami da Shagari sun cigaba da caccakar shugabanni, babu wanda zai ga mutuncinsu.

"Ina tunanin yana jin dadin abinda yake yi. Yana neman a sauraresa kuma a yaba masa a kan miyagun maganganunsa."

A yayin tabbatar da cewa Najeriya tana da matsala kuma dole a shawo kanta, Ogbeh ya ce: "Ina mutunta Obasanjo, yana da kaifin basira amma ya gujewa kalubale mara tushe."

Idan za mu tuna, tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ya sake sukar Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari inda ya ce ƙasar ta kama hanyar lalacewa kuma kawunnan yan kasar sun rabu.

Obasanjo ya yi wannan furucin ne yayin jawabin da ya yi a wurin wani taron da kungiyoyi masu wakiltan yankunan kasar suka hallarta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel