Yanzu-yanzu: Gamayyar Ma'aikatan Lafiya a Najeriya sun shiga yajin aiki

Yanzu-yanzu: Gamayyar Ma'aikatan Lafiya a Najeriya sun shiga yajin aiki

- Bayan janye yajin aiki Likitoci, sauran ma'aikatan kiwon lafiya sun yi yaji

- Sun bayyana cewa gwamnati tana nuna banbanci tsakaninsu da Likitoci

- Ma'aikatan sun hada da malaman lafiya, unguzoma, masu karantar da ilmin kiwon lafiya dss

Gamayyar ma'aikatan lafiya a Najeriya wato JOHESU ta umurci mambobinta su ajiye aiki saboda za'a shiga yajin aiki fari daga karfe 12 na daren Lahadi, 3 ga watan Satumba, 2020.

An yanke shawarar haka a zaman majalisar zartaswar gamayyar da akayi ranar Asabar.

A wasikar da JOHESU ta aikewa Ministan kwadago ranar Lahadi, ta ce ta baiwa gwamnatin tarayya talalan mako daya domin magance matsalolin amma babu abinda aka cimma.

Ma'aikatan kiwon lafiyan suna bukatar gwamnatin tarayya ta biyasu kudin alawus na mambobinta.

Hakazalika ta bukaci gwamnati ta gyara albashinsu, ta dabbaka hukuncin kotun ma'aikata kuma ta biya bashin albashin da ma'aikata ke binta.

KU KARANTA:Motar haya ta yi kicibis da motar 'Daf', an rasa rayuka (Bidiyo)

A cewar wasikar: "Za ka tuna cewa a ganawar da mukayi a ofishinka ranar Alhamis, 10 ga watan Satumba, 2020, JOHESU ta bukaci sa'o'i 48 domin martani bayan mun tattauna yadda mukayi da gwamnatin tarayya ga majalisar zartaswa."

"Saboda haka, mun yi zaman majalisar zartaswarmu yau (Asabar), 12 ga Satumba, 2020. A karshen zaman,.....mun yanke shawaran cewa mambobinmu zasu janye daga aiki tun da gwamnatin tarayya ta ki biyan bukatunmu."

Yanzu-yanzu: Gamayyar Ma'aikatan Lafiya a Najeriya sun shiga yajin aiki

Yanzu-yanzu: Gamayyar Ma'aikatan Lafiya a Najeriya sun shiga yajin aiki
Source: Facebook

A bangare guda, Kungiyar Likitoci masu neman kwarewa a Najeriya NARD ta dakatad da yajin aikin da ta tafi sakamakon rashin cimma matsaya da gwamnatin tarayya da kudaden alawus din mambobinta.

Shugaban kungiyar, Dr Aliyu Sokomba, ya tabbatar da hakan ga tsahar Channels da yammacin Alhamis.

Sokomba ya bayyana cewa kungiyar za ta cigaba da tattaunawa da gwamnatin tarayya bayan makonni biyu.

A ranar Laraba, gwamnatin tarayya da Likitoci sun cimma matsaya domin kawo karshen yajin aikin.

A ganawar da aka kwashe kwana daya ana yi, wakilan likitocin sun bayyana cewa zasu tattauna da majalisar zartaswar kungiyar domin ganin yiwuwar janye yajin aikin.

Bayan zaman ranar Laraba, gwamnatin tarayya ta ce zata kara musu N8.9 billion matsayin kudin alawus na COVID19 na watan Yuni ga dukkan Likitocin Najeriya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel