Atiku ya yi ta’aziyya ga Sanata Wamakko kan mutuwar ‘yarsa

Atiku ya yi ta’aziyya ga Sanata Wamakko kan mutuwar ‘yarsa

- Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya yi wa Sanata Wamakko ta’aziyyar mutuwar ‘yarsa

- Tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi addu’an Allah ya ba iyalan juriya

- Babban jigon APC, Bola Tinubu ma ya ziyarci tsohon gwamnan domin yi masa ta’aziyya

Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar, ya mika ta’aziyyar sa ga tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aliyu Magatakarda Wamakko, kan rasuwar ‘yarsa mai shekaru 23, Sadiya Magatakarda Wamakko.

Wamakko ya kasance shugaban kwamitin majalisar dattawa kan tsaro.

A bisa ga jaridar The Nation, Sadiya ta rasu a daren ranar Alhamis, 10 ga watan Satumba, a asibitin koyarwa na jami’ar Danfodio, Sokoto, wajen haihuwa.

Marigayiya Sadiya ta mutu ta bar iyayenta, mijinta, Tambari Yusuf Arkilla, ma’aikacin hukumar NPA, Lagos da kuma yarinya ‘yar shekara biyar.

Atiku ya yi ta’aziyya ga Sanata Wamakko kan mutuwar ‘yarsa

Atiku ya yi ta’aziyya ga Sanata Wamakko kan mutuwar ‘yarsa Hoto: Atiku Abubakar/Daily Post
Source: UGC

KU KARANTA KUMA: 2023: An kaddamar da yakin neman zaben shugabancin kasa na Tinubu

Da yake martani kan mummunan al’amarin, Atiku ya ce: “Mutuwar Sadiya Magatakarda Wamakko a wajen haihuwa abun bakin ciki ne. A matsayin mutum na uba, yana da matukar ciwo rasa ‘ya.

“A madadina da iyalaina, Ina mika ta’aziyya ga Sanata Aliyu Wamakko da iyalansa kan wannan rashi. Ina addu’an Allah ya basu juriya. Allah ya ji kanta da rahama sannan ya sa a tuna da ita na alkhairi.”

Babban jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Bola Tinubu ma ya ziyarci tsohon gwamnan domin yi masa ta’aziyya.

KU KARANTA KUMA: Gamayyar dattawa da matasan Arewa mazauna jihar Edo sun alanta goyon bayansu Osaze Ize-Iyamu (Hotuna da Bidiyo)

A wani labarin mun kawo maku a baya cewa tsohon mataimakin shugaban Nigeria, Atiku Abubakar ya sanar da rasuwar surukarsa kuma matar marigayi Lamido Aliyu Musdafa, Hajiya Khadija Aliyu Musdafa.

Hajiya Musdafa ta rasu ne a ranar Litinin, kuma mataimakin shugaban kasar ya misaltata da mace mai kirki da dattako.

An binne ta a ranar Talata a garin Yola, babban birnin jihar Adamawa, kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.

Dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP a zaben 2019 ya aika da sakon ta'aziyyarsa ga iyalan Lamidon Adamawa, HRH Muhammadu Barkindo Aliyu Musdafa da kuma iyalan gidan Musdafa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel