2023: An kaddamar da yakin neman zaben shugabancin kasa na Tinubu

2023: An kaddamar da yakin neman zaben shugabancin kasa na Tinubu

- Wata kungiyar magoya bayan Dr Ahmed Bola Tinubu, shugaba kuma jigon jam'iyyar APC ta kaddamar da yakin fara neman zabensa

- Kungiyar ta kaddamar da yakin neman zabensa shugaban kasa a 2023 a karkashin jam'iyyar APC a garin Abuja

- Kamar yadda shugaban kungiyar ya sanar, babu shakka Tinubu yayi an gani kuma zai dasa daga inda Buhari zai tsaya a 2023

Wata kungiyar siyasa mai suna BAT 23, ta kaddamar da yakin neman zabe da kuma tattara masoya ga shugaban jam'iyyar APC, Bola Tinubu a zaben shugabancin kasa da ke zuwa na 2023 a Abuja.

An gano cewa, Tinubu na kokarin fitowa takarar zaben shugaban kasa a karkashin jam'iyyar APC a kasar nan.

Shugaban kungiyar, Umar Inusa, a yayin kaddamar da fara yakin neman zaben a Abuja a ranar sati, ya ce BAT 23 ta hada da dukkan magoya bayan Tinubu daga jihohi 36 na kasar nan tare da birnin tarayya, Abuja.

KU KARANTA: Bidiyo: Ina son kasancewa da shi har abada - Mahaifiya mai soyayya da danta

2023: An kaddamar da yakin neman zaben shugabancin kasa na Tinubu
2023: An kaddamar da yakin neman zaben shugabancin kasa na Tinubu. Hoto daga Daily Trust
Asali: UGC

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Makarantar horon hafsoshin 'yan sanda ta saka ranar jarabawar shiga

Inusa ya yi bayanin cewa, an kafa kungiyar domin kafa Tinubu kafin zuwan zaben shugabancin kasa na 2023.

Ya ce Tinubu gogaggen shugaba ne wanda yake da kwarewar siyasa da zai iya dasawa daga inda shugaban kasa Muhammadu Buhari zai tsaya a 2023.

"Tinubu shugaba ne wanda ke mayar da ba komai zuwa komai, kuma yana gamsar da jama'arsa da abinda yake da shi.

"A zamaninsa na gwamnan jihar Legas, albashin ma'aikata, ayyukan cigaba da na taimako duk basu taba yankewa ba.

"Idan yayi hakan a Legas kuma bamu taba jin cewa jihar Legas ta fada karayar tattalin arziki ba a wancan lokacin, idan ya samu dukkan kasar nan yana kula da ita, ya kenan?

"Mu duba wannan bangaren farko. Wannan shine irin mutumin da muke fatan ya shugabancemu kuma muke goyon bayansa domin sauya akalar kasar nan," yace.

Tinubu daga yankin kudu maso yamma na Najeriya, ya dade da fara tsara yadda zai zama shugaban kasa.

Ya goyi bayan wannan gwamnatin tun daga farkonta, kuma ana tsammanin za a saka masa ta hanyar zabensa a karkashin jam'iyyar a 2023.

Jam'iyyarsa ta APC tana tunani tare da saka da warwarar yadda za a yi mulkin karba-karba da yankin kudancin kasar nan bayan mulkin shugaba Buhari a karo na biyu, wanda dan arewa ne daga jihar Katsina.

Tuni jam'iyyun siyasa suka karba salon karba-karba na tsawon shekaru domin tabbatar da cewa shugabancin kasa ya dinga kaiwa da kawowa tsakanin yankunan arewa da kudu.

A wani labari na daban, gamayyar dattawa da matasan Arewa mazauna jihar Edo bayyana goyon bayansu ga dan takarar kujeran gwamnan jihar karkashin jam'iyyar All Progressives Congress APC, Fasto Osaze Ize-Iyamu, TVC ta ruwaito.

Hakan ya gudana ne yau Asabar, 12 ga watan Satumba, 2020 yayinda Sanata Ibrahim Shekarau yake jihar domin yiwa APC yakin neman zabe.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
APC
Online view pixel