An kashe ƴan bindiga a Kaduna, an kama ƴan aikensu da N1.5m a Zamfara - Sojoji

An kashe ƴan bindiga a Kaduna, an kama ƴan aikensu da N1.5m a Zamfara - Sojoji

- Dakarun sojojin Najeriya sun yi nasarar kashe yan bindiga da dama tare da kama ƴan saƙon su

- Sojojin sun samun wannan nasarorin ne a hare-haren da suka kai maɓuyar ƴan ta'addan bayan samun sahihan bayanan sirri

- Sojojin sun kuma yi nasarar kama ƴan saƙon ƴan bindiga da kudi masu yawa da masu yi musu leƙen asiri

Dakarun sojoji na Operation Thunder Strike sun kashe ƴan bindiga masa yawa sun kuma lalata sansanin su a dajin Kuduru da Kuyambana a jihar Kaduna.

Sojin sun sama wannan nasarorin ne bayan samun sahihan bayanan sirri da ke nuna yan bindigan na amfani da wuraren domin shirya kai hari.

An kashe ƴan bindiga a Kaduna, an kama ƴan saƙonsu da N1.5m a Zamfara - Sojoji

An kashe ƴan bindiga a Kaduna, an kama ƴan saƙonsu da N1.5m a Zamfara - Sojoji. Hoto daga The Punch
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Allah ya yi wa ƴar Sanata Wamakko rasuwa a Sokoto

Sojin sun kuma kama wadanda ake zargin ƴan saƙon ƴan bindigan ne da kudi Naira miliyan 1.565 a ƙaramar hukumar Maru da ke jihar Zamfara a ranar 7 ga watan Satumba.

Kakakin Hedkwatan Tsaro, Manjo Janar John Enenche ya kuma ce sojojin tare da hadin gwiwan ƴan banga sun kama ƴan leƙen asirin yan bindiga a ƙaramar hukumar Faskari a Katsina sun kuma kashe wasu biyu a Samawa da ke ƙaramar hukumar Bungudu a Zamfara.

Da ya ke jawabi a kan ayyukan sojoji a Abuja a ranar Alhamis, ya ƙara da cewa dakarun Operation Thunder Strike a Jeka Da Rabi a hanyar Kaduna - Abuja sun kashe ƴan bindiga 4 sun kwato bindigu.

Har wa yau, ya ce wani ɗan bindiga mai suna Sada ya mika wuya tare da AK-47 uku, sub-machine gun da alburusai ga sojoji a Dansadau a Zamfara.

Kazalika, Dakarun Hadarin Daji a ranar 6 ga watan Satumba a Koha a ƙaramar hukumar Batsari a Katsina sun kama yan bindiga 6.

KU KARANTA: Bidiyo: Ban taɓa sanin wani lokaci da al'ummar musulmi suka shiga halin ƙunci kamar yanzu ba - Goron-Dutse

Bugu da ƙari, a ranar 7 ga watan Satumba sojoji a Kekuwuje a ƙaramar hukumar Maru na jihar Zamfara sun kama ƴan saƙon ƴan bindiga dauke da N1,565,550.

Ya ƙara da cewa, "Yayin arangama da suka yi, sojoji sun kashe ɗan ta'adda guda sun ƙwato bindigu 3. Duk dai a ranar, soji sun kama yan Boko Haram biyu a Kamuya a ƙaramar hukumar Biu, da wani Usman Almajiri a Damaturu a Yobe."

A wani rahoton daban, kun ji cewa Rundunar Ƴan sandan jihar Katsina sun kama wani hatsabibin mai garkuwa da mutane, Abubakar Ibrahim a dajin Rugu da ke jihar.

An kuma ceto mutum uku da ya yi garkuwa da su bayan kama mai garkuwa da ake zargin yana cikin ƙungiyar masu satar mutane da ke adabar mutane a ƙananan hukumomin Batsari, Safana, Ɗan Musa da Kurfi a jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel