Zaben Edo: Rundunar 'yan sanda ta tura DIG, AIG, Kwamishinoni 8 (Sunayensu)

Zaben Edo: Rundunar 'yan sanda ta tura DIG, AIG, Kwamishinoni 8 (Sunayensu)

> Ranar 19 ga watan Satumba hukumar zabe ta kasa (INEC) ta tsayar domin gudanar da zaben gwamna a jihar Edo

> IGP Mohammed Adamu, babban sifeton rundunar 'yan sanda, ya tura wasu manyan jami'ai domin su tabbatar da tsaro a jihar Edo

> Manyan jami'an da rundunar 'yan sanda ta tura sun hada da DIG guda daya, AIG guda daya, da kwamishinoni guda 8

Babban sifeton rundunar 'yan sandan Najeriya (IGP), Mohammed Adamu, ya tura wasu manyan jami'an 'yan sanda zuwa jihar Edo domin su saka ido a kan zaben kujerar gwamna mai zuwa.

Tuni hukumar zabe ta kasa (INEC) ta tsayar da ranar 19 ga watan Satumba domin gudanar da zaben kujerar gwamnan jihar Edo.

Babban mataimakin sifeton rundunar 'yan sanda (DIG), Adeleye Olusola Oyabade, ne jagoran tawagar manyan jami'an da IGP Adamu ya tura.

DCP Frank Mba, kakakin rundunar 'yan sanda na kasa, ya ce; AIG Hosea Hassan zai kasance mataimaki ga DIG Oyabade.

A cikin wata sanarwa da DCP Mba ya fitar yau, Juma'a, rundunar 'yan sanda ta bayyana cewa aikin manyan jami'an shine tabbatar da tsaro a jihar Edo.

Zaben Edo: Rundunar 'yan sanda ta tura DIG, AIG, Kwamishinoni 8 (Sunayensu)
IGP Mohammed Adamu
Asali: Twitter

Rundunar 'yan sanda ta ce ta dorawa tawagar alhakin tabbatar da ganin cewa an gudanar da zaben jihar Edo cikin lumana.

DUBA WANNAN: Shugaban kasa Buhari: Noma shi ne mafita ga matasa masu jini a jika

DUBA WANNAN: Zaben Edo: Kwankwaso ya fadi dalilin kai ziyararsa Benin da kuma irin nasarorin da ya samu

"Sauran manyan jami'an 'yan sanda da ke cikin tawagar sun hada da CP Garba Baba Umar, CP Habu Sani, CP Buba Sanusi da CP Akeera M. Yonous.

"Sauran hudun sune; CP Omololu S. Bishi, CP Abutu Yaro, CP Philip Aliyu Ogbadu da CP Olokade T. Olawale," a cewar sanarwar mai dauke da sa hannun DCP Mba.

Sanarwar ta kara da cewa za a bawa kowanne daya daga cikin manyan jami'an bangaren aikin da zai mayar da hankali a kansa.

Kazalika, IGP Adamu ya bukaci jami'an 'yan sanda da ke aiki da manyan mutane su kauracewa raka iyayen gidansu zuwa wurin kada kuri'a a ranar zabe.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel