An kama wani da yayi shekaru 2 yana karbar albashin kwamishina a Niger

An kama wani da yayi shekaru 2 yana karbar albashin kwamishina a Niger

- An gano ma'aikata da dama da suke karbar albashin da ya ɗara matsayinsu a jihar Niger

- Cikin wadanda aka gano har da masinja mai karɓar albashin babban alƙali da wani mai karɓar albashin kwamishina

- Aikin tantancewar da gwamnatin Niger ta yi ya saka an bankaɗo masu laifuka da dama kuma an kori wasu daga cikinsu

Gwamnan jihar Niger ta gano ma'aikatan jihar da dama da suka tafka magudi su ke biyan kansu albashin da ya fi ƙarfin aikinsu.

Aikin tantance wa da gwamnatin jihar ta gudanar ne yasa asirin waɗannan ma'aikatan ya tonu.

Kwamishinan bogi ya shafe shekaru biyu yana karɓar albashi a jihar Niger
Kwamishinan bogi ya shafe shekaru biyu yana karɓar albashi a jihar Niger. Hoto daga LIB
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Bidiyo: Ban taɓa sanin wani lokaci da al'ummar musulmi suka shiga halin ƙunci kamar yanzu ba - Goron-Dutse

Shugaban ma'aikatan jihar, wacce ta sanar da hakan a ranar Alhamis 11 ga watan Satumba ta ce cikin wadanda aka gano har da masinja mai karɓar albashin babban alƙali da kwamishinan noma na bogi da ya yi shekaru 2 yana karɓar albashi.

An sallami ma'aikata da dama a jihar bayan tantancewar kuma an gano ma'aikatar kula da lafiya na jihar ne ta fi tara balagurbin ma'aikata.

Sauran wuraren da aka samu masu laifin sun hada da makarantun horas da ma'aikatan jinya na koyar da kimiyyar lafiya, ma'aikatan ilimi, shari'a da makarantar koyon aikin unguwar zoma.

KU KARANTA: Allah ya yi wa ƴar Sanata Wamakko rasuwa a Sokoto

Kwamishinan noma na jihar, Haruna Dukku ya ce ba domin tantancewar ba da za ayi kuskuren zargin shi ke karbar albashi biyu.

Dukku ya ce;

"Wani ya shafe shekaru biyu yana karɓar albashin kwamishinan aikin noma.

"Hakan yasa za a ga kamar ina karɓar albashi biyu ne. Idan da ba a gano wannan abin ba me zan ce idan a ƙarshen wa'addi ne EFCC sun zo gida na sun ƙwankwasa ƙofa?"

Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Laraba ya kafa wata kwamiti da za ta cigaba da jan ragamar bunkasa tattalin arzikin ƙasar mai suna Agenda 2050.

Wannan kwamitin za ta ɗora ne a kan tsarin tattalin arziki na vision 2020 da tsohon shugaban kasar Musa Yar'adua ya kaddamar da wasu tsare tsaren.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel