Ambaliya a jihar Bauchi: Mutane 16 sun mutu, gidaje 2000 sun salwanta

Ambaliya a jihar Bauchi: Mutane 16 sun mutu, gidaje 2000 sun salwanta

- Jihar Bauchi ta fuskanci ambaliya ruwa a kananan hukumomi 11 a shekarar nan

- Hukumar SEMA ta bayyana cewa mutane sun rasa muhallansu sama da 2000

- Yayinda ake ambaliya a Arewa, mutan Kudu na addu'an Allah ya kawo musu ruwa

Akalla mutane 16 sun rasa rayukansu yayinda gidaje 2,000 suka salwanta sakamakon annobar ambaliyar ruwan sama a jihar Bauchi a shekarar 2020.

A rahoton da Jaridar Punch ta yi, an yi ambaliya a kananan hukumomin jihar da dama.

Hukumar agajin gaggawa ta jihar Bauchi ta tabbatar da hakan a hirarta da Punch ranar Juma'a.

Sakataren din-din-din hukumar SEMA, Habu Ningi, ya ce ambaliyar ta shafi garuruwa 11 a kananan hukumomi fiye da goma.

Yace, "Mun ziyarci dukkan wuraren da ambaliyar bana ta shafa. Kawo yanzu mun samu rahotanni 11 a kananan hukumomi 11 na jihar.

"Zuwa yanzu, mutane 16 sun rasa rayukansu, 11 a karamar hukumar Bauchi, 1 a karamar hukumar Warji, 2 a karamar hukumar Shira, 2 a karamar hukumar Dambam."

"Sama da gidaje 2,000 sun ruguje sakamakon ambaliyar. An asarar amfani gona a gonaki 1,117."

"Gwamnatin jihar ta taimakawa mutanen da wannan abu ya shafa da kayayyaki domin rage radadin annobar."

Ningi ya shawarci mazauna su daina gina gidaje a magudanar ruwa kuma su daina zuba shara a cikin rafuka.

DUBA WANNAN: Wasu yan iska na shirya yadda wani tsohon gwamna zai gaji Buhari - Kabiru Marafa

Ambaliya a jihar Bauchi: Mutane 16 sun mutu, gidaje 2000 sun salwanta
Ambaliya a jihar Bauchi: Mutane 16 sun mutu, gidaje 2000 sun salwanta
Asali: UGC

A ranar Laraba ne shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya fitar da sakon jaje ga jama'ar jihar Kebbi a kan asarar rayuka da amfanin gona da ambaliyar ruwa ta haifar a jihar.

Da ya ke mika sakon ta'aziyya ga wadanda su ka rasa wasu nasu sakamakon ambaliyar, Buhari ya bayyana cewa asarar kayan amfanin gona za ta shafi wadatuwar kayan abincin da ake nomawa a gida Najeriya.

Buhari ya bayyana hakan ne a cikin jawabin da ya fitar ta hannun babban kakakinsa, Malam Garba Shehu.

"Shugaba Buhari ya jajantawa jama'ar jihar Kebbi da ambaliyar ruwa ta halaka 'yan uwansu tare da lalata musu gonakinsu." Yace

Ambaliyar ruwan sama ta yi sanadiyar mutuwar mutane 6 tare da lalata gonakin dumbin manoma a jihar Kebbi.

An yi kiyasin cewa ambaliyar ruwan ta lalata amfanin gona na biliyoyin Naira.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel