Zaben Edo: Kwankwaso ya fadi dalilin kai ziyararsa Benin da nasarorin da ya samu

Zaben Edo: Kwankwaso ya fadi dalilin kai ziyararsa Benin da nasarorin da ya samu

> Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, tsohon gwamnan jihar Kano, ya kai ziyarar aiki zuwa jihar Edo

> Jam'iyyar PDP ce ta tura Sanata Kwanso zuwa Edo domin ya taya gwamnan jihar, Godwin Obaseki, yakin neman zabe

> Ranar 19 ga wata hukumar zzabe ta kasa (INEC) ta tsayar domin gudanar da zaben gwamnan a jihar Edo

A ranar Alhamis, 10 ga watan Satumba, ne tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwanwaso, ya sanar da cewa ya na jihar Edo domin gabatar da wani aiki na musamman da jam'iyyar PDP ta turashi ya gudanar.

A ranar Asabar, 19 ga wata, za a gudanar zaben gwamna a jihar Edo, kamar yadda hukumar zabe ta kasa (INEC) ta dade da sanarwa.

A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na tuwita a ranar Juma'a, Sanata Kwankwaso, ya bayyana cewa ya jagoranci gudanar da tarurruka tsakanin mutanen arewa da ke zaune a Edo da gwamnan jihar, Gowin Obaseki.

"A cigaba da shirin tunkarar zaben gwamnan Edo, na jagoranci gwamna Obaseki da mataimakinsa, Phliph Shuaibu, wajen ganawa da kungiyoyin 'yan arewa daban-daban da ke zaune a fadin jihar Edo.

"Dukkan wadannan kungiyoyi da suka hada da na addinai da al'adu, 'yan kasuwa da fatake da sauransu, sun goyi bayan takarar gwamna Obaseki a karkashin inuwar jam'iyyar PDP.

"Mun samu hadin kai da goyon bayan dukkan kungiyoyin 'yan arewa mazauna jihar Edo, wanda hakan manuniyace cewa nasara ta gwamna Obaseki ce a zaben kujerar gwmnan jihar Edo da za a gudanar ranar 19 ga wata," a cewar Kwankwaso.

Zaben Edo: Kwankwaso ya fadi dalilin kai ziyararsa Benin da nasarorin da ya samu

Kwankwaso
Source: Twitter

Legit.ng Hausa ta wallafa cewa wasu gungun mutanen Arewa da ke zaune a jihar Edo sun tabbatar da goyon bayansu ga tazarcen mai girma gwamna Godwin Obaseki na jam’iyyar PDP.

Sakataren mai girma Sarkin Hausawan Benin, Mohammed Baba, ya bayyana cewa kuri’arsu ta na wurin PDP a zaben gwamnan da za ayi a jihar Edo.

Jaridar Vanguard ta ce wadannan Hausawa da ke zaune a garin Benin sun ce, “Ba mu da zabi illa mu goyi bayan PDP a zaben 19 ga watan Satumban 2020.”

KARANTA: Tashin farashin man fetur da lantarki: Shawarar da Kwankwaso ya bawa Buhari

KARANTA: Janye tallafin man fetur: Gwamnatin tarayya ta fadi ayyukan da zata yi da kudaden

Tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso, Jakadanmu ne. Ya fada mana mu zabi Gwamna Obaseki, kuma hakan za mu yi.” Inji Mohammed Baba.

Game da wannan ra’ayi, sakataren shugaban Hausawan ya bayyana cewa su na daukar Sanata Kwankwaso a matsayin Jagorarsu, kuma su na girmama shi.

Haka zalika wasu Musulmai a karkashin tafiyar “Edo Muslims for Peace and Unity” sun bayyana cewa za su kadawa Godwin Obaseki da Philip Shaibu kuri’arsu.

Zaben Edo: Kwankwaso ya fadi dalilin kai ziyararsa Benin da nasarorin da ya samu

Kwankwaso da Obaseki
Source: Twitter

Zaben Edo: Kwankwaso ya fadi dalilin kai ziyararsa Benin da nasarorin da ya samu

Kwankwaso da Philiph Shaibu
Source: Twitter

Zaben Edo: Kwankwaso ya fadi dalilin kai ziyararsa Benin da nasarorin da ya samu

Kwankwaso a wurin taro 'yna raew mazauna jihar Edo
Source: Twitter

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel