An kama hatsabibin mai garkuwa da mutane a Katsina (Hoto)

An kama hatsabibin mai garkuwa da mutane a Katsina (Hoto)

- Yan sanda a jihar Katsina sun yi nasarar kama wani gawurtaccen mai garkuwa da mutane a jihar

- An kama Abubakar Ibrahim ne a dajin Rugu da ke Katsina bayan ya karɓi kuɗin fansa daga iyalan wasu da ya sace

- Yan sandan SARS da suka damƙe shi sun kuma ceto wasu da ya yi garkuwa da su tare da kudin fansa N241,000 da ya ƙarba

Rundunar Ƴan sandan jihar Katsina sun kama wani hatsabibin mai garkuwa da mutane, Abubakar Ibrahim a dajin Rugu da ke jihar.

An kuma ceto mutum uku da ya yi garkuwa da su bayan kama mai garkuwa da ake zargin yana cikin ƙungiyar masu satar mutane da ke adabar mutane a ƙananan hukumomin Batsari, Safana, Ɗan Musa da Kurfi a jihar.

An kama hatsabibin mai garkuwa da mutane a Katsina (Hoto)

An kama hatsabibin mai garkuwa da mutane a Katsina (Hoto). Hoto daga LIB
Source: Twitter

DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun kama kayan tallafin korona na jihar Benue da aka sayar a kasuwar Kano

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Gambo Isah ne ya bayar da wannan sanarwar kamar yadda LIB ya ruwaito.

Kakakin ya kuma ce wanda aka kama ɗin ya bayyana cewa shine ya yi wa wasu ƴan bindiga jagoranci a ranar 7 ga watan Satumba suka kai hari a ƙauyukan Dagarawa da Kudewa a ƙananan hukumomin Safana da Kurfi a jihar.

Ibrahim ya amsa cewa shine ya yi garkuwa da Ashiru Ibrahim mai shekaru 32, Duduwa Audu mai shekaru 50, da Asiya Saleh mai shekaru 45 a ƙauyen Kudewa a ƙaramar hukumar Kurfi ya kai su dajin Ruga.

An kuma kwato kuɗin fansa N241,000 da ya karba bayan sace su.

Kakakin ƴan sandan ya ce;

KU KARANTA: Bidiyo: Ban taɓa sanin wani lokaci da al'ummar musulmi suka shiga halin ƙunci kamar yanzu ba - Goron-Dutse

"Asarin sa ya tonu ne a lokacin da aka ɗana masa tarko kuma ya faɗa sannan jami'an SARS suka kama shi bayan ya karɓi kuɗin fansa N241,000 daga hannun yan uwan wanda ya yi garkuwa da su.

"A ranar 10 ga watan Satumban 2020 misalin ƙarfe 9.30 na safe yan sanda suka yi nasarar kama shi kuma suka ceto wadanda ya yi garkuwa da su."

A wani rahoton daban, kun ji ofishin hukumar yaƙi da masu yi wa arzikin ƙasa ta'annati, EFCC, ta fara bincike a kan wani da ake zargin ɗan damfara ne da aka kama ya ɓoye katim ATM 2,886 da layyukan waya hudu cikin taliyar indomie.

Jami'an hukumar Kwastam ne suka mika wanda ake zargin, Ishaq Abubakar ga hukumar EFCC a ranar Alhamis 10 ga watan Satumban 2020 domin a bincike shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel