Sai muna kwance ni da ita sai ta sulale zuwa dakin wani gardi suyi iskanci - Malamin Islamiyya ya kai matar shi kara kotu

Sai muna kwance ni da ita sai ta sulale zuwa dakin wani gardi suyi iskanci - Malamin Islamiyya ya kai matar shi kara kotu

- Miji ya bayyanawa kotu cewa ya sha kama matarsa a lokuta da dama tana guduwa dakin makocinsu tana kwanciya da su

- Sai dai matar ta karyata wannan zargi inda ta bayyanawa alkalin mugayen halayen mijin nata

- A karshe alkalin ya raba auren ma'auratan ya kuma bukaci matar ta rike yaran da suka haifa guda biyu

A ranar Alhamis ne 10 ga watan Satumba, wani Malamin Islamiyya dake zaune a Ibadan mai suna, Naheem Salami, ya bayyanawa wata kotu dake a Ibadan, jihar Oyo, cewa matarshi mai suna Taiwo, tana sulalewa daga kan gadonsu a lokacin da suke kwance da daddare, tana zuwa dakin makwabcinsu wanda yake gwauro ne ba shi da aure.

Salami, wanda ya isa kotu a bisa karar shi da Taiwo ta kai gaban kotu akan a raba aurensu, ya bayyana cewa matarshi muguwar mata ce.

Amma Malamin Islamiyyar ya ce yaki amincewa da kotun ta raba auren, saboda yaran da suke da su, wadanda suka samu ta hanyar wannan aure, da kuma abinda ya kira da kokarin da yake yi na ganin bai batawa iyayenta rai ba.

Sai muna kwance ni da ita sai ta sulale zuwa dakin wani gardi suyi iskanci - Malamin Islamiyya ya kai matar shi kara kotu
Sai muna kwance ni da ita sai ta sulale zuwa dakin wani gardi suyi iskanci - Cewar Malamin Islamiyya da matar shi kara gaban kotu
Asali: Facebook

"Ya mai shari'a, babban dalilin da ya sanya nake dukan Taiwo shine, a duk lokacin da muke kwance akan gado, tana sulalewa daga kan gadonmu da muke kwance ta gudu dakin wani makwabcinmu da yake zaune babu aure. Nayi mata gargadi akan ta daina zuwa taki dainawa.

"Nayi alkawarin ba zan kara dukanta ba, har limamin mu na aika mata domin yayi mata nasiha, amma Taiwo taki daina zuwa dakin wannan mutumi," cewar shi.

KU KARANTA: Tirkashi: An dakatar da daurin aure bayan wani mutumi ya shiga wajen daurin aure yace shine mahaifin amarya da ango

Matar ta bayyanawa kotu cewa ta gaji da auren, inda ta zargi mijinta akan cewa yana dukanta har yayi mata tsirara wani lokacin.

Ta ce: "Yana yawan dukana, hatta lokacin da nake da ciki ya dake ni, har na haihu, lokacin ina mai jego, yana zagina tare da iyayena baki daya. Yana yawan yi mini barazana, idan har na sake barin gidan shi. Sai da aka yi mini tiyata aka ciro jaririn dana haifa, amma yaki biyan kudin wannan tiyata da maganin. Iyayena ne suka biya kudin.

"A lokacin dana bar gidan shi, na tafi da yarana, na saka su a makarantar kudi, amma yazo gidan mahaifina ya dauke su ta karfin tsiya. Ya mayar da su makarantar gwamnati, inda hakan yana bata mini rai sosai. Da yaga cewa na san makarantar da suke ya canja musu zuwa wata makarantar gwamnatin.

"Ya'yana suna shan wahala sosai a gidan nan. Ya mai shari'a, idan kaga yaran zaka gane cewa suna shan wahala. Ina so na dauki nauyinsu domin su samu su rayu. Karshen gani na da su suna cikin wahala da yunwa. Ya mai shari'a ka taimaka ka kwato mini yarana. Bai taba kama ni da kowa ba kamar yadda ya fada. Karya yake yi. Ba shi da tsoron Allah ko kadan."

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kashe manoma 2 a jihar Nasarawa

Alkalin kotun, Cif Odunade Ademola, ya ce zargin da Tawio take yi ga mijinta Salami na raba aure gaskiya ne, kuma yana mamakin abinda ya sanya yake rokon kada a raba auren.

A karshe dai alkalin kotun ya raba auren, ya kuma bayar da yaran guda biyu ga mahaifiyarsu domin ta cigaba da daukar nauyinsu.

Haka kuma wata mata ta zargi mijinta mai suna Adewunmi Adewale da sanya ta zubar da ciki har 15 wanda ta dauka, amma daga bisani sai ya barta tare da yaranta uku a gidan haya ba tare da kula ba.

Sukurat ta ce bincikenta ya nuna cewa Adewale ya auri wasu mata biyu daga wurare daban-daban a garin Ibadan, kuma ta roki kotun da ta bata rikon 'ya'yansu uku.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng