Kana taka Allah na tashi: Ango ya mutu kwanaki kadan bayan ya auri kyakkyawar amaryar shi

Kana taka Allah na tashi: Ango ya mutu kwanaki kadan bayan ya auri kyakkyawar amaryar shi

- Wani saurayi dan Najeriya mai suna Rex Ebube Amatu, ya mutu bayan auren shi da wata budurwa sanadiyyar hatsarin babur

- An ruwaito cewa lamarin ya faru a Asaba

- Mutane da yawa sun nuna jimaminsu akan wannan mutuwa tashi yayin da hotunanshi dana amaryar shi ke ta yawo a shafukan sadarwa

Rana ce ta bakin ciki ga iyalan Rex Ebube Amatu, yayin da ya mutu a ranar Talata 8 ga watan Satumba, 2020, sakamakon hatsarin babur da ya rutsa da shi.

A yadda rahotanni suka nuna Ebube ya mutu kwanaki kadan bayan auren shi da wata kyakkyawar budurwa. Mutumin dan asalin jihar Anambra ne.

An ruwaito cewa hatsarin ya faru a Asaba a lokacin da yake komawa gidanshi dake Legas. Wani mai amfani da shafin sadarwa na Facebook mai suna Ben Chiedo ya ce lamarin ya faru yayin da katuwar mota ta bi ta kan angon.

Kana taka Allah na tashi: Ango ya mutu kwanaki kadan bayan ya auri kyakkyawar amaryar shi
Hoto dake nuna angon da amaryar shi a lokacin da aka daura musu aure | Source: Facebook
Asali: Facebook

An ruwaito cewa tuni kyakkyawar matarshi na dauke da ciki. Mutane da yawa da suka ji wannan labari sun nuna rashin jin dadinsu akan abinda ya faru da wadannan ma'aurata.

KU KARANTA: Za'a yiwa daliban jihar Ogun karin aji kai tsaye ba tare da sun zana jarrabawa ba idan suka koma makaranta a ranar 21 ga watan Satumba - Dapo Abiodun

Ga dai wasu daga cikin abubuwan da mutane ke cewa kan wannan lamari:

KU KARANTA: Hotuna: Magoya bayan APC sun ragargza shagunan wasu 'yan kasuwa da suka koma PDP

Wani mai suna Kene Kay cewa yayi: "Menene haka, abin tausayi. Allah ka bawa 'yan uwa da matar wannan mutumi juriyar rashin shi, Allah kuma ya jikan shi. Amen."

A wani labari kuwa da Legit.ng ta kawo muku, an dakatar da daurin auren wasu masoya a Jihar River, bayan wani mutumi ya fito ya bayyana cewa shine mahaifin amaryar da angon, a yayin da ake shirin daura auren.

Anne Magwi da Jotham Munini, wadanda ya kamata a daura aurensu a ranar Asabar, 5 ga watan Satumba, an ruwaito cewa iyayensu daya.

Sai dai kuma a wani rahoto da jaridar The Nation ta ruwaito, ya nuna yadda mahaifinsu tare da 'yan uwanshi suka isa wajen daurin auren, suka dakatar da daurin auren.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng