A karon farko an rubuta jarrabawar WAEC a garin Chibok shekaru 6 bayan sace dalibai mata da Boko Haram suka yi a garin

A karon farko an rubuta jarrabawar WAEC a garin Chibok shekaru 6 bayan sace dalibai mata da Boko Haram suka yi a garin

- An gabatar da jarrabawar WAEC a karon farko a garin Chibok, bayan shekaru shida da sace 'yammatan Chibok

- Sama da 'yammata 200 'yan ta'adda suka sace a garin na Chibok a shekarar 2014

- Wasu daga cikin 'yammatan da aka sace din an ceto su, inda wasu kuma har yanzu suke hannun 'yan ta'addar

Bayan shekaru shida da sace sama da dalibai 200 a makarantar mata ta Chibok, an gabatar da jarrabawar kammala sakandare ta WAEC a karon farko a garin.

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa makarantun sakandare na Chibok dake jihar Borno an basu damar gabatar da jarrabawar ta WAEC.

Legit.ng ta gano cewa wani babban jami'in hukumar soja ne mai suna Abdul-Khalifa Ibrahim, ya bayyana haka a lokacin da yake karbar bakuncin ziyarar wasu mambobi na kungiyar ilimi mai suna (EiEWG) a ranar Alhamis, 10 ga watan Satumba, a garin Maiduguri, jihar Borno.

Idan ba a manta ba a shekarar 2014 aka rufe duka makarantu a Chibok, bayan 'yan ta'addar Boko Haram sun sace dalibai mata sama da 200.

A karon farko an rubuta jarrabawar WAEC a garin Chibok shekaru 6 bayan sace dalibai mata da Boko Haram suka yi a garin
Dalibai suna rubuta jarrabawar WAEC a Chibok, jihar Borno, shekaru 6 bayan harin 'yan Boko Haram
Asali: UGC

Idan ba a manta ba a yayin da gwamnatin tarayya ta samu nasarar kwato wasu daga cikin daliban, wasu daga cikinsu har yanzu suna hannun 'yan Boko Haram din.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kashe manoma 2 a jihar Nasarawa

Ibrahim wanda yake shine kwamandan rundunar soji ta sashe na 1, ta Operation Lafiya Dole, ya samu wakilcin Ifeanyi Otu, shugaban ma'aikatan rundunar sojin.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN), ya bayyana illar da kungiyar 'yan ta'addar ta yiwa fannin ilimi a yankin Arewa maso Gabas, inda ya bayyana cewa yanzu komai ya koma daidai a yankin.

"Abin farin ciki ne ace a karon farko, bayan shekaru 6, an rubuta jarrabawar WAEC a Chibok ta hanyar jami'an tsaro da suka taimaka.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun tare matafiya, sun yi garkuwa da 20 daga ciki a Katsina

"Duka mu shaida ne akan abinda ya faru a shekarun baya da ya hada da sace 'yan matan Chibok, yanka dalibai a Buni Yadi, da kuma sace dalibai a Dapchi. Wadannan duka sun faru kuma mun dauki darasi a kansu.

"Bari na bayyana cewa shugaban hukumar soji yana matukar kokari a bangaren ilimi ta hanyar aika malamai makarantu a yankin Arewa maso Gabas.

"Mun tabbatar da cewa komai yana dawowa daidai a fannin ilimi a yankin nan kamar yadda duka muka sani, ilimi shine hasken rayuwa. Tun a farko da ba a samu irin wannan matsalar ba, amma saboda rashin ilimi yayi yawa a wannan yanki ya sanya matsalar ta samo asali," ya ce.

Legit.ng kuma ta kawo muku rahoton yadda gwamnatin jihar Ogun ta umarci makarantu a jihar da su bude a ranar 21 ga watan Satumba a zango na farko na shekarar 2020/2021.

Gwamnatin ta kara cewa hakan ya biyo bayan komawar da daliban ajin karshe na sakandare suka yi kwanan nan, wadanda a halin yanzu suke zana jarrabawar WAEC.

Kunle Somorin, wanda yake shine sakataren yada labarai na gwamnan jihar Dapo Abiodun, ya bayyana cewa wannan bude makarantu da za ayi za'a bude ga duka daliban firamare, sakandare, kwaleji, da kuma makarantun gaba da sakandare.

Haka kuma gwamnatin ta bayyana shirinta na yiwa dalibai karin aji kai tsaye ba tare da sun rubuta wata jarrabawa ba a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel