Kuyi haƙuri: Tsadar kayan abinci na ɗan ƙaramin lokaci ne - Gambari

Kuyi haƙuri: Tsadar kayan abinci na ɗan ƙaramin lokaci ne - Gambari

- Shugaban ma'aikatan shugaban kasa, Ibrahim Gambari ya bukaci yan Najeriya da su kara hakuri kan tashin farashin kayan abinci

- Ya ce tsadar kayan masarufin na dan lokaci ne domin a cewarsa sun fara sauka saboda shigowar sabbin hatsi kasuwa

- Shugaba Muhammadu Buhari ma ya ce gwamnatinsa na kokarin bunkasa yankin domin samar da abinci yadda ya kamata

Ibrahim Gambari, Shugaban ma’aikatan Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce tashin farashin kayayyakin abinci na ɗan ƙaramin lokaci ne.

Ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, a lokacin taron kungiyar tsaron abinci ta kasa, wanda aka gudanar a fadar Shugaban kasa da ke Abuja, jaridar The Cable ta ruwaito.

Gambari, wanda ya bayyana cewa farashin hatsi a yan baya-bayan nan ya nuna cewa ya sauka sosai, ya ce ragin zai karade fadin kasar yayinda ake fito da sabbin hatsi kasuwa.

KU KARANTA KUMA: NSCDC ta kama magidanci kan kashe dan matarsa a jihar Jigawa

“Tashin farashin kayan abinci na baya-bayan nan na barazanar kawo karancin abinci a Najeriya,” in ji shi.

“Jiya, ofishina a matsayinta na sakatariya, kungiyar tsaron abinci ta kasa, mun gana da kungiyoyin masu sayar da kayan abinci domin gano abin da ya kawo tashin farashin kayan masarufi da kuma gano dabarun yi wa tufkar hanci.

“Duk da cewar an bayyana wasu dalilai da suka haddasa tsadar kayayyakin, an sanar damu cewa tsadar na raguwa saboda shigowar sabbin hatsin da ake girbewa.

“Misali, sabon maasara wanda ake siyar da buhu kan N25,000 a kwanaki yanzu ana siyar dashi tsakanin N12,000 da N17,000, kuma ana sanya ran zai fadi zuwa tsakanin N7,000 da N8,000 kan kowani buhu a watan Nuwamban 2020, a cewar shugabannin kungiyar kayan masarufi. An kuma samu ragi a farashin gero, wake da dawa. Don haka a kalli tashin farashin a matsayin na dan lokaci,” inji shi.

Kuyi haƙuri: Tsadar kayan abinci na ɗan ƙaramin lokaci ne - Gambari
Kuyi haƙuri: Tsadar kayan abinci na ɗan ƙaramin lokaci ne - Gambari Hoto: The Cable
Source: UGC

Gambari ya jaddada muhimmancin hadin kan masu ruwa da tsaki domin shawo kan matsalar da ke tunkarowa musamman a wannan lokaci da ake fama da matsalar COVID-19 da karancin ababen more rayuwa.

Ya kuma bukaci mahalarta taron da su hadu su yi aiki kafa-da-kafa domin tabbatar da samuwar isasshen abinci.

“Noma babban abun da gwamnati ta ba wa muhimmanci ne sannan yana da tasiri wurin kawo cigaban kasa”, inji shi.

Da yake jawabi kan kokarin tabbatar da tsaron abinci, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi bayanin cewa gwamnatinsa ta mayar da hankali sosai wajen habbaka fannin domin samar da abinci mai dorewa.

KU KARANTA KUMA: Hotuna: Kunkuru mai shekaru 80 da mota ta taka ya rayu

A wani labarin kuma, mun ji cewa Kungiyar masu gidajen burodi guda biyu, PBAN da kuma AMBCN, sun koka kan yadda farashin kayan da suke sarrafa burodin ya tashi a kasuwa.

Kungiyoyin, a taron manema labarai a Lagos, sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta duba tashin farashin kayan masarufin, don daukar matakin ragewa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel