Yanzu-yanzu: Ana shirin zama, gobara ta kama ofishin hukumar INEC (Hotuna)

Yanzu-yanzu: Ana shirin zama, gobara ta kama ofishin hukumar INEC (Hotuna)

Ofishin hukumar gudanar da zaben kasa mai zaman kanta INEC dake Akure, birnin jihar Ondo na ci bal-bal yanzu haka.

Hukumar INEC ta bayyana cewa gobarar ta lalata kayayyakin zabe.

Hakazalika ba'a san abinda ya haddasa gobarar ba har yanzu.

Wannan gobara na zuwa ne saura wata daya zaben gwamnan jihar da aka shirya ranar 10 ga watan Oktoba, 2020.

A jawabin da kakakin hukumar, Barista Festus Okoye, ya saki, ya ce wutar ta kona kwantenan da aka ajiye na'u'rorin Card Reader.

Ya ce za'a kaddamar da bincike ba tare da bata lokaci ba idan aka kammala kashe wutar.

Jawabin yace: "Gobara ta barke yau, Alhamis, 10 ga Satumba, 2020 a hedkwatar hukumar INEC dake Akure. Wutar ta kona kwantenan da aka ajiye na'urorin Card Reader misalin karfe 7:30 na dare."

"Yanzu haka jami'an kwana-kwana na kokarin kashe wutar."

"Kwamishanan yada labarai na hukumar, Festus Okoye, wanda yake jihar Ondo yanzu domin shirye-shiryen zaben da aka shirya yi ranar 10 ga watan Oktoba, 2020 ya garzaya ofishin misalin karfe 8."

Kalli hotunan:

Yanzu-yanzu: Ana shirin zama, gobara ta kama ofishin hukumar INEC
Yanzu-yanzu: Ana shirin zama, gobara ta kama ofishin hukumar INEC
Asali: Twitter

KU KARANTA WANNAN: Macijiya ta gantsari matashi a azzakari sai da ya kusa bakuntan lahira

Yanzu-yanzu: Ana shirin zama, gobara ta kama ofishin hukumar INEC
Yanzu-yanzu: Ana shirin zama, gobara ta kama ofishin hukumar INEC
Asali: Twitter

KU DUBA NAN: Yanzu-yanzu: Likitocin Najeriya sun janye yajin aiki, zasu koma bakin aiki

A bangare guda, Shugaban Alkalan Najeriya, Alkali Tanko Mohammed, ya rantsar da Alkalai 85 domin zama a kotun zabukan gwamnan da zasu gudana a jihar Edo da Ondo da kuma na maye gurbin yan majalisa da suka mutu a sassan Najeriya.

Kotun daukaka kara ce hedkwatar sauraron karan zabe kuma shugabar kotun, Alkali Monica Dongban-Mensem, ce ke da hakkin zaben Alkalan da zasu zauna kan kowani kara.

Za'a gudanar da zaben jihar Edo ranar 19 ga Satumba, 2020, yayinda za'ayi na jihar Ondo ranar 10 ga Oktoba, 2020.

Bayan zaben da sanar da wanda yayi nasara, duk dan takaran da bai amince da sakamakon ba na da kwanaki 21 domin shigar da kara kotun zabe.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel