'Yan bindiga sun kashe manoma 2 a jihar Nasarawa

'Yan bindiga sun kashe manoma 2 a jihar Nasarawa

- Rundunar 'yan sandan jihar Nasarawa ta tabbatar da kisan gillar da aka yi wa wasu manoma biyu a garin Kadarko

- An gano cewa, makiyaya ne suka samu manoman har gona a ranar Alhamis inda suka yi musu kisan gilla

- Kakakin rundunar 'yan sandan jihar ya ce tuni sun suka tura jami'an tsaro domin su mamaye yankin domin gujewa martani

Wasu 'yan bindiga wadanda ba a san ko su waye ba, sun halaka manoma biyu a jihar Nasarawa. Ana zargin makiyaya ne suka shiga kauyen Icenyam da ke yankin Kadarko Olive a karamar hukumar Keana ta jihar.

Bayanan da aka samu duk da babu yawa a kan harin sun bayyana cewa, 'yan bindigar sun samu manoman a yayin da suke gonakinsu, Vanguard ta wallafa.

Rundunar 'yan sandan jihar ta tabbatar da aukuwar lamarin. Kamar yadda kakakin rundunar, ASP Rahman Nansel ya sanar a wata tattaunawa, ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Ya ce tuni rundunar suka tura jami'anta domin tabbatar da zaman lafiya a yankin tare da gujewa mayar da amartani.

Titus Chahur, wanda ya samu zantawa da manema labarai a garin Kadarko, ya yi kira ga gwamnatin jihar da su gaggauta kawo karshe kashe-kashen da suka yi kamari a yankin.

KU KARANTA: Tirkashi: An dakatar da daurin aure bayan wani mutumi ya shiga wajen daurin aure yace shine mahaifin amarya da ango

'Yan bindiga sun kashe manoma 2 a jihar Nasarawa
'Yan bindiga sun kashe manoma 2 a jihar Nasarawa. Hoto daga Vanguard
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yadda 'yan sanda suka azabtar da budurwa mai shekaru 20 har ta mutu

A wani labari na daban, 'yan bindiga sun kai farmaki garin Tungan Maje, waje-wajen birnin tarayya Abuja, inda sukayi awon gaba da mutane da ba'a san yawansu ba har yanzu.

Premium Times ta samu labari daga wani mazaunin garin cewa akalla mutane 20 aka sace bayan dogon lokaci ana harbe-harbe a cikin garin.

Kakakin hukumar yan sandan birnin tarayya, Anguri Manzah ya bayyanawa wakilin Premium Times cewa bai yi jawabi a kai ba tukun amma yana shirin yi. Bai tabbatar da adadin wadanda aka sace ba, ko kuma akwai wadanda suka mutu ko suka samu rauni.

Wani mazaunin unguwar da aka sakaye sunansa ya ce sun fara jin harbe-harben bindiga ne misalin karfe 12:15 na dare kuma sai da aka kwashe awa daya ana yi. Ya ce an galabi yan bangan dake garin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel