Da duminsa: An garkame zauren majalisar Ondo, an hana 'yan majalisar shiga
- A yau Alhamis, jami'an tsaro da ke gadin kofar shiga majalisar jihar Ondo sun hana 'yan majalisar shiga
- Kamar yadda bidiyon ya bayyana mai tsawon minti daya da sakan 30, an ga 'yan majalisar suna zanga-zangar abinda ya faru
- Sun bayyana rashin jin dadinsu, amma kuma jami'an tsaro sun ce wannan umarni ne daga kakakin majalisar
An samu wani lamari mai kama da wasan kwaikwayo a kofar shiga majalisar zartarwa ta jihar Ondo, yayin da 'yan majalisa biyu na jam'iyyar adawa suka hana sauran 'yan majalisa shiga zauren majalisar.
Wannan lamarin an nade shi a wani bidiyo mai tsayin minti daya da sakan 30, kuma ya yadu a kafafen sada zumuntar zamani.
Jaridar The Punch ta gano cewa lamarin ya faru a ranar Alhamis.
'Yan majalisar da abinda ya faru da su sune Festus Akingbaso mai wakiltar yankin Akoko ta arewa maso gabas da Rasheed Elegbeye mai wakiltar mazabar Idanre.
A bidiyon, an ga 'yaan majalisar suna zanga-zanga a kan abinda 'yan sandan kofar shiga majalisar suka yi musu.
Jami'an tsaro da ke kofar shiga majalisar sun tabbatar da cewa, wannan umarni ne daga kakakin majalisar, Bamidele Oloyeloogun.
Amma daya daga cikin 'yan majalisar sun kira kakakin majalisar, Bamidele Oloyelogun, wanda ya sanar da shi abinda ke faruwa a kofar shiga majalisar.
Daya daga cikin fusatattun 'yan majalisar, Elegbeleye, ya tabbatar da hakan a bidiyon inda yace wannan abun da ya faru an yi shi ne da gangan.
Karin bayani na nan tafe...
KU KARANTA: Gwamnan APC da sojin Najeriya sun yi musayar kalamai, sun yi wa juna kaca-kaca
KU KARANTA: PDP ta zabga babbar asara a jihar Bauchi, jigonta ya bi Dogara APC
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng