Yanzu; 'Yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zanga a kan kara farashin mai, sun kama wasu

Yanzu; 'Yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zanga a kan kara farashin mai, sun kama wasu

> Mambobin jam'iyyar SPN tare da wasu sauran matasa a jihar Legas sun shirya zanga-zangar nuna rashin amincewa da karin farashin mai da wutar lantarki

> Sai dai, jami'an 'yan sanda sun tarwatsa gungun matasan tare da kama wasu daga cikin jagororin zanga-zangar

> Har yanzu 'yan Najeriya a fusace suke da gwamnati saboda karin wutar lantarki da farashin litar mai

Jami'an rundunar 'yan sanda sun kama wasu daga cikin masu zanga-zangar nuna rashin amincewa da karin farashin man fetur.

An kama masu zanga-zangar ne a yau, Alhamis, a yankin Ojuelegba da ke garin Legas.

Jaridar Punch ta rawaito cewa bayan masu zanga-zangar da aka kama, an kwace kayan aikin 'yan jaridu.

Daya daga cikin jagororin masu zanga-zangar, Hassan Soweto, ya ce an kama mutane 18 da suka hada da 'yan jarida.

DUBA WANNAN: Hukumar kwastam ta samu fiye da biliyan ₦9 a cikin wata 8

"An kama mu tare da 'yan jarida da mambobin jam'iyyar SPN da safiyar yau (Alhamis) yayin da muka fito zanga-zangar nuna rashin amincewa da karin farashin man fetur da kudin wutar lantarki.

"A yanzu haka da nake rubuta wannan sako ina kulle a bayan motar 'yan sanda a hanyar zuwa hedikwatarsu," a cewar Soweto, shugaban matasan SPN.

KARANTA WANNAN: Shugaba Buhari ya jagoranci taron majalisar wadatar da kasa da abinci

Yanzu; 'Yan sanda sun tarwatsa asu zanga-zanga a kan kara farashin mai, sun kama wasu
Yanzu; 'Yan sanda sun tarwatsa asu zanga-zanga a kan kara farashin mai, sun kama wasu
Source: Twitter

Yanzu; 'Yan sanda sun tarwatsa asu zanga-zanga a kan kara farashin mai, sun kama wasu
Yanzu; 'Yan sanda sun tarwatsa asu zanga-zanga a kan kara farashin mai, sun kama wasu
Source: Twitter

Yanzu; 'Yan sanda sun tarwatsa asu zanga-zanga a kan kara farashin mai, sun kama wasu
Ma su zanga-zanga
Source: Twitter

A wani labarin, hukumar hana fasa kwauri ta kasa wacce aka fi sani da 'Kwastam' ta samu rabanu na biliyan ₦976.6 daga watan Janairu zuwa Agusta na shekarar 2020.

A wata takarda da kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya wallafa ranar Alhamis, an nuna cewa an samu kudaden ne daga rabanu a kan kayan da aka shigo dasu Najeriya da kudin duti da sauransu.

NAN ta bayyana cewa takardar ta fito ne daga ofishin hulda da jama'a na hukumar kwastam. Kididdiga ta nuna cewa kudaden da hukumar Kwastam ta samu daga rabanu a kan kayan da aka shigo dasu basu taba kaiwa yawan na wannan karon ba.

Alkaluma sun nuna cewa kudaden haraji da aka kara a kan kaya (VAT) sune ke bin bayan yawan kudin da hukumar ta samu daga rabanu a kan shigo da kaya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel