Yanzu-yanzu: Makarantar horon hafsoshin 'yan sanda ta saka ranar jarabawar shiga

Yanzu-yanzu: Makarantar horon hafsoshin 'yan sanda ta saka ranar jarabawar shiga

- Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta sanar da ranar jarabawar shiga makarantar horon hafsin 'yan sanda da ke Wudil, jihar Kano

- An saka ranar Alhamis 17 ga watan Satumban 2020 a matsayin ranar da za ayi jarabawar a dukkan fadin Najeriya

- Za a yi jarabawa ga mazauna Kaduna da kewaye a makarantar horar da malamai da ke kan babban titin Kaduna zuwa Zaria

Hukumar 'yan sanda a jihar Kaduna, ta ce an saka ranar jarabawar shiga makarantar horon hafsin 'yan sanda da ke Wudil a jihar Kano domin diban dalibai karo na takwas.

An saka za a yi jarabawar a ranar Alhamis, 17 ga watan Satumban 2020 a dukkan fadin kasar nan, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige, ya bayyana haka a wata takarda da ya fitar a ranar Alhamis a garin Kaduna.

Kamar yadda yace, ana tsammanin masu rubuta jarabawar zasu zauna a kwalejin horar da malaman makaranta (NTI) da ke kan babbar hanyar Kaduna zuwa Zaria.

KU KARANTA: Matashi ya kashe mahaifiyarsa a kan ruwan lemo da kuma motarta

Yanzu-yanzu: Makarantar horon hafsoshin 'yan sanda ta saka ranar jarabawar shiga
Yanzu-yanzu: Makarantar horon hafsoshin 'yan sanda ta saka ranar jarabawar shiga. Hoto daga Daily Nigerian
Source: Twitter

KU KARANTA: Da duminsa: Sabbin mutum 176 sun sake harbuwa da korona a Najeriya

"Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna tana sanar da jama'a, ballantana mazauna jihar Kaduna, cewa za a yi jarabawar shiga makarantar horar da hafsin 'yan sanda da ke Wudil a ranar 17 ga watan Satumba a fadin kasar nan.

"Rundunar tana sanar da wadanda suka cike fom da su fitar da shi domin shiga jarabawar a ranar," yace.

A wani labari na daban, babban sifeton rundunar 'yan sandan Najeriya (IGP), Mohammed Adamu, ya roki sarakunan gargajiya su bawa gwamnati goyon baya a kokarinta na ganin bayan fashi da makami, garkuwa da mutane, barnar 'yan bindiga, da satar shanu.

Mista Adamu, wanda kwamishinan 'yan sandan jihar Neja, Adamu Usman, ya wakilta, ya bayyana hakan ne yayin ganawa da ma su rike da sarautun gargajiya na masarautar Kontagora.

An yi muhimmiyar ganawa a tsakanin rundunar 'yan sanda da ma su rike da sarautar gargajiya a masarautar Kontagora domin tattauna yadda za a samu nasarar tabbatar da tsaro a tsakanin al'umma.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel