Vision 2050: Buhari ya kafa kwamtin bunkasa tattalin arzikin kasa

Vision 2050: Buhari ya kafa kwamtin bunkasa tattalin arzikin kasa

Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Laraba ya kafa wata kwamiti da za ta cigaba da jan ragamar bunkasa tattalin arzikin ƙasar mai suna Agenda 2050.

Wannan kwamitin za ta ɗora ne a kan tsarin tattalin arziki na vision 2020 da tsohon shugaban kasar Musa Yar'adua ya kaddamar da wasu tsare tsaren.

Ɗan kasuwa Mista Atedo Peterside da ministan kuɗi, kasafi da tsare-tsare, Zainab Ahmed ne za su jagoranci kwamitin kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Vision 2050: Buhari ya kafa kwamitin farfaɗo da tattalin arziki
Vision 2050: Buhari ya kafa kwamitin farfaɗo da tattalin arziki
Source: Facebook

DUBA WANNAN: Fittacen fasto na ƙasar Ghana ya bindige matarsa har lahira a Amurka

Mashawarcin shugaban kasa na musamman, Femi Adesina ya bayyana hakan cikin wata sanarwa mai taken "Agenda 2050: Shugaba Buhari ya kafa kwamitin jagorancin ƙasa da za ta yi aiki don tsamo ƴan Najeriya miliyan 100 daga talauci zuwa shekarar 2030."

"Babban aikin wannan kwamitin shine tsamo yan Najeriya miliyan 100 daga talauci cikin shekaru 10 duba da cewa hasashen Bankin Duniya ya ce yawan mutanen Najeriya zai haura miliyan 400 zuwa shekarar 2050," kamar yadda Adesina ya ruwaito Buhari ya ce.

Buhari ya ce ya zama dole a samu wani shirin da zai maye gurbin Vision 2020 da ERGP domin tabbatar da ingantaccen cigaba da tsari a kasar.

Shugaba Buhari ya ce yana sa ran kwamitin zai taka muhimmiyar rawa wurin fitar da tsare tsare da shawarwari da yadda za a aiwatar da su domin inganta tattalin arziki a kasar.

KU KARANTA: Garba Shehu: An sayar da man fetur N600 kowanne lita a mulkin PDP

Ya ƙara da cewa yana fatar kwamitin za ta cigaba da aiki ko bayan wa'adin mulkinsa ya ƙare nan da shekaru uku.

Har wa yau, shugaban kasar ya shawarci mambobin kwamitin su kasance masu jajircewa da sadaukar da kai a wurin gudanar da ayyukan su.

A wani labarin daban, kun ji kwamishinan ma'adinai, man fetur da iskar gas na jihar Edo, Joseph Ikpea ya yi murabus daga gwamnatin Gwamna Godwin Obaseki.

Ikpea ya yi murabus ɗin ne a ranar 9 ga watan Satumban shekarar 2020 kamar yadda LIB ta ruwaito.

Kwamishinan da ya ajiye aikinsa kwanaki 10 kafin zaben gwamna a jihar ya bayyana dalilin da yasa ya yi hakan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel