Kwamishina ya yi murabus kwanaki 10 kafin zaɓe a Edo

Kwamishina ya yi murabus kwanaki 10 kafin zaɓe a Edo

Kwamishinan ma'adinai, man fetur da iskar gas na jihar Edo, Joseph Ikpea ya yi murabus daga gwamnatin Gwamna Godwin Obaseki.

Ikpea ya yi murabus ɗin ne a ranar 9 ga watan Satumban shekarar 2020 kamar yadda LIB ta ruwaito.

Kwamishinan da ya ajiye aikinsa kwanaki 10 kafin zaben gwamna a jihar ya bayyana dalilin da yasa ya yi hakan.

Kwamishina ya yi murabus kwanaki 10 kafin zaɓe a Edo
Kwamishina ya yi murabus kwanaki 10 kafin zaɓe a Edo. Hoto daga LIB
Asali: Twitter

Ya ce ba zai iya watsi da jam'iyyar All Progressives Congress, APC, da ya taimaka aka gina ta ba a ƙaramar hukumar Esan ta kudu na jihar.

DUBA WANNAN: Bidiyo: Amarya ta fasa auren mijinta a lokacin da aka tafi wurin daurin aure

Ikpea shine kwamishina na uku da ya yi murabus daga gwamnatin Godwin Obaseki.

Ga abinda ya rubuta a wasikar ajiye aikinsa;

"Na rubuta wannan ne domin sanar da kai yin murabus daga muƙami na. Ina son mika godiya ta ga mai girma Mista Godwin Obaseki saboda damar da ya bani na yin aiki a matsayin kwamishinan ma'adinai, man fetur da iskar gas ƙarƙashin gwamnatinsa.

"Ɗaya daga cikin dalilan da yasa nayi murabus shine dama ita siyasa ana gina ta ne a kan ra'ayi, yarda da juna da girmama juna, amma kawo yanzu ban ga hakan ba kuma bana tsamanin lamarin zai canja a gaba.

KU KARANTA: Fittacen fasto na ƙasar Ghana ya bindige matarsa har lahira a Amurka

"Baya ga haka, ina daga cikin wadanda suka kawo jam'iyyar APC zuwa ƙaramar hukumar Esan ta Kudu kuma fiye da kashi 90 cikin dari na magoya baya na ƴan APC ne saboda haka akwai wahala in bar gidan da na gina da hannu na.

"Kazalika, gwamnatin ba ta girmama matsayi na domin duk da ni kwamishina ne daga wurin shugaban ƙaramar hukuma ko hadiman gwamna na ke samun bayanai.

"Zan cigaba da bawa mai girma gwamna goyon baya na a duk lokacin da buƙatar hakan ta taso. Ina maka fatan nasara a duk harkokin ka na rayuwa."

A wani labarin daban, Legit.ng ta ruwaito cewa Garba Shehu, Mai magana da yawun shugaba Muhammadu Buhari ya yi martani a kan ƙarin kuɗin man fetur inda ya ce an siya man fetur fiye da farashin sa na yanzu a lokacin mulkin jam'iyyar PDP.

A rubutun da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Talata, mai magana da yawun shugaban kasar ya ce har Naira 600 an siya litar man fetur a zamanin mulkin PDP.

Gwamnatin Tarayya tayi amfani da Hukumar Tallata Albarkatun Man Fetur, PPMC, a baya bayan nan ta ƙara farashin man fetur ga masu sari daga N138.62 zuwa N151.56 duk lita.

Bayan ƙarin kuɗin man fetur ɗin, ƴan kasuwa sun yi ƙarin kuɗin litar man fetur daga Naira 148 zuwa Naira 158 zuwa Naira 162 duk lita.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel