Bidiyon wani yaro da yake yiwa mahaifiyarshi bayanin yadda ya kamu da son wata budurwa ya bawa mutane mamaki

Bidiyon wani yaro da yake yiwa mahaifiyarshi bayanin yadda ya kamu da son wata budurwa ya bawa mutane mamaki

- Wani bidiyo na ta yawo na wani yaro da yake bayyana yadda ya kamu da soyayya

- Karamin yaron kyakkyawa ya bayyanawa mahaifiyarshi yadda budurwar shi ta ci amanarshi

- Wannan bidiyo dai ya yadu sosai a shafukan sadarwa na kasar Afrika ta Kudu

Wani yaro karami ya koyi darasi dake nuni da cewa soyayya tana iya cutar da yara kanana. Ba a kowanne lokaci bane muke dacewa da mutanen da muke so ba.

Wani karamin yaro da mahaifiyarshi ta dauki bidiyon a lokacin da yake yi mata bayani akan yadda budurwarshi ta guje shi.

Bidiyon wanda aka wallafa a shafin sadarwa na Twitter mai suna @aypee_madicks, yaron ya bayyana yadda budurwar shin ta guje shi ta komawa wani.

KU KARANTA: Alkali ya sanya barawo ya share kotu baki daya bayan kama shi da laifin sata

Bidiyon wani yaro da yake yiwa mahaifiyarshi bayanin yadda ya kamu da son wata budurwa ya bawa mutane mamaki
Karamin yaro ya bayyanawa mahaifiyarshi yadda soyayya ta juya masa baya | Photo Source: @aypee_madicks/Twitter
Source: UGC

"Mum, kinga wannan yarinyar da nake so, Ta daina soyayya dani yanzu. Tana son sabon yaron yanzu," ya sanarwa da mahaifiyar shi sunan yaron.

Mahaifiyar yaron ta tambayeshi idan babu matsala, inda yaron ya girgiza kan shi, alamun babu.

KU KARANTA: An kama mutane biyu da suka kaiwa Hausawa hari a jihar Rivers

Mahaifiyar ta sake tambayarshi idan yayi magana da yarinyar da kuma yaron, sai ya ce:

"Ta ce ba ta sona yanzu kwata-kwata."

Ga dai bidiyon yadda hirar su ta wakana, wanda aka wallafa a shafin Twitter:

Wannan bidiyo ya jawo mutane sunyi ta maganganu a kanshi, inda mutanen kasar Afrika ta Kudu suka taya wannan kyakkyawan karamin yaro jimami.

Haka kuma wani yaro mai shekaru 11 mai suna PJ Brewer-Laye, ya zama jan gwarzo bayan da ya dauka matakin da kowanne mai hankali zai iya dauka wurin ceto rayuwar kakarsa mai suna Angela.

Kakarsa ta fara korafin jiri, rashin karfin jiki da kuma disashewar gani, amma babu wanda zai taimaka a gidan.

Kamar yadda jaridar New York Post ta wallafa, a lokacin da tsohuwar ta fara jin jikinta babu dadi, ta fito inda ta jingina da wata alama da ke kan titi sannan jikanta da ke wasa ya hangota.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel