Gwamnan APC da sojin Najeriya sun yi musayar kalamai, sun yi wa juna kaca-kaca

Gwamnan APC da sojin Najeriya sun yi musayar kalamai, sun yi wa juna kaca-kaca

An samu rikici tsakanin gwamnatin jihar Benue da hukumomin sojin Najeriya inda suka yi musayar kalamai a kan kisan shugaban 'yan tawayen da sojin suka kashe a ranar Talata.

Shugaban 'yan tawayen mai suna Terwase, wanda aka fi sani da Gana, yana cikin jerin mutanen da gwamnati ta kwashe shekaru hudu tana nema ido rufe.

A ranar Talata, Gana ya shirya mika kansa domin samun rangwame tare da 'yan kungiyarsa a hannun Gwamna Samuel Ortom da jami'an tsaron jihar, jaridar Vanguard ta wallafa.

A daren Talata, Gwamna Ortom ya tabbatar da cewa wasu sojoji sun yi awon gaba da 'yan tawayen, wadanda suka damke a babbar hanyar Makurdi zuwa Gboko a yayin da suke hanyarsu ta zuwa Makurdi domin mika wuya.

An gano cewa, hankali ya tashi a jihar bayan da kwamandan rundunar Operation Whirl Stroke, Manjo Janar Adeyemi Yekini ya tabbatar da cewa dakarun sojin sun kama tsagerun.

KU KARANTA: Malami ya sanar da abinda zai yi idan aka gayyacesa shaida a gaban kwamitin binciken Magu

Gwamnan APC da sojin Najeriya sun yi musayar kalamai, sun yi wa juna kaca-kaca
Gwamnan APC da sojin Najeriya sun yi musayar kalamai, sun yi wa juna kaca-kaca. Hoto daga Vanguard
Asali: Twitter

KU KARANTA: NLC ga Lai Mohammed: Ba kudin man fetur muke korafi ba, karancin albashi ne matsalarmu

Amma kuma, a daren Talata, hukumomin sojin Najeriya sun ce sun samu babbar nasara a yaki da garkuwa da mutane, fashi da makami da kuma harin 'yan tawaye a yankin arewa ta tsakiya ta Najeriya.

Hakan ya biyo bayan halaka babban dan ta'addan da aka dade ana nema kuma shugaban tsagerun da ke assasa miyagun ayyuka a jihohin Benue da Taraba.

Sai dai, Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue a jiya ya ce yana bukatar bayani daga hukumonin soji, saboda ya yi matukar mamakin dalilin da yasa suka kashe Gana.

Gwamnan yace, "Na yi matukar mamaki kuma na tsorata da naji cewa sojin Najeriya sun kashe Gana. Saboda an gano cewa sun kama shi a ranar Talata.

"Da kaina na kira kwamandan OPWS, wanda yace min suna aiki ne amma zai kira ni daga baya. Amma babu dadewa suka saki takardar da ke bayyana cewa sun kashe shi."

A takardar da Gwamnan ya fitar, ya ce wannan wata hanya ce ta toshe zaman lafiya da hukumomin suka yi a jiharsa saboda dai Gana na kan hanyarsa ne ta mika wuyansa da tuba.

Legit.ng ta ruwaito cewa, dubun Shahararren dan bindigan da aka dade ana nema ruwa a jallo, Terwase Agwaza Gana, ya shiga hannun jami'an Sojin 'Special forces' a jihar Benue, TVC ta ruwaito.

Kwamandan 4 Special Forces Command, Doma, jihar Nasarawa, Maj. -Gen. Moundhey Ali, ya bayyanawa manema labarai ranar Laraba cewa an kashe Gana ne a hanyar Gbese-Gboko-Makurdi bayan musayar wuta.

Yace, "Misalin karfe 12:00 na ranar Talata, mun samu labarin shahrarren dan bindiga Terwase Akwaza Agbadu wanda aka fi sani da Gana na hanyar Gbese-Gboko-Makurdi.

"Dakarun rundunar Operation ‘Ayem Akpatuma III’ suka bazama tare hanyar. Misalin karfe 13:00, an yi musayar wuta tsakanin Soji da Gana inda aka kasheshi."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel