Alkali ya sanya barawo ya share kotu baki daya bayan kama shi da laifin sata

Alkali ya sanya barawo ya share kotu baki daya bayan kama shi da laifin sata

- Wani barawo da aka gurfanar a gaban alkali an bukaci ya share farfajiyar kotu na tsawon kwana biyu

- Barawon dai wanda aka dauke shi aikin direba, yayi yunkurin sacewa wanda ya dauke shi aikin injin shara

- Lamarin dai ya faru a babban birnin tarayya Abuja

A jiya Laraba ne, 9 ga watan Satumba, 2020, wata kotun majistire dake Wuse Zone Six, babban birnin tarayya Abuja, ta umarci wani direba mai suna Ahmed Danladi, mai shekaru 35, da ya share cikin kotu na tsawon kwana biyu bisa kama shi da laifin sata.

'Yan sanda sun kama Danladi dake zaune a No 44 Oran Street, Wuse Zone One, Abuja, da laifin sata.

Alkali ya sanya barawo ya share kotu baki daya bayan kama shi da laifin sata
Alkali ya sanya barawo ya share kotu na tsawon kwana biyu | Photo source: Daily Trust
Source: Twitter

Alkalin kotun majistiren, Omolola Akindele, ya umarci mai laifin ya dinga zuwa kotun ya dinga yin shara na tsawon kwanaki biyu, bayan an same shi da wannan laifi, inda aka yanke masa hukunci ba tare da an ciyo shi tara ba.

KU KARANTA: Suna shan wiwi saboda su fatattaki miyagun aljanu - Lauya ya kare matasa 3 a kotu

Dan sandan da ya gurfanar da shi a gaban kotun, ASP Peter Ejike, ya sanar da kotun cewa, mutumin da aka yiwa satar mai suna Samuel Joseph, wanda yake zaune waje daya da Danladi, ya kai kara zuwa ofishin 'yan sanda na Wuse Zone 3 a ranar 1 ga watan Satumba.

Ejike ya ce mutumin wanda Joseph ya dauka a matsayin direba, a wannan rana ya dauke mishi injin shara, wanda ba a bayyana ainahin kudin shi ba, sannan yayi kokarin mika shi ga wani ta katanga domin ya gudu da shi.

KU KARANTA: Dan Najeriya da ya ki karbar cin hancin $6m ya samu lambar yabo

Dan sandan ya bayyana cewa bayan sun gabatar da bincike a kanshi, ya amsa laifinsa.

Ya ce wannan laifi ya sabawa sashe na 289 na kundin tsarin mulki. Kamar dai yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito.

Haka kuma Legit.ng ta kawo muku rahoton yadda wata mata ta zargi mijinta mai suna Adewunmi Adewale da sanya ta zubar da ciki har 15 wanda ta dauka, amma daga bisani sai ya barta tare da yaranta uku a gidan haya ba tare da kula ba.

Sukurat ta ce bincikenta ya nuna cewa Adewale ya auri wasu mata biyu daga wurare daban-daban a garin Ibadan, kuma ta roki kotun da ta bata rikon 'ya'yansu uku.

Sukurat wacce take martani a kan bukatar sakin da Adewale ya mika gaban kotun, ta ce mijinta ya saba barinsu sai ciwo ya samesa ya dawo mata gida.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel