An kama jaruma Rhea Chakbraborty kan laifin samar wa tsohon saurayinta jarumi Sushant Singh Rajput miyagun kwayoyi

An kama jaruma Rhea Chakbraborty kan laifin samar wa tsohon saurayinta jarumi Sushant Singh Rajput miyagun kwayoyi

An kama jarumar Bollywood Rhea Chakraborty a ranar Talata 8 ga watan Satumba bayan an ce ta amsa cewa tana kungiyar wasu masu safarar miyagun kwayoyi kuma ta kan samar wa jarumi Sushant Singh Rajput kwayoyi.

Jarumi Singh Rajput ya rasu sakamakon cututuka masu alaka da ta'amulli da miyagun kwayoyi.

Jarumar da hukumar yaki da ta'amulli da miyagun kwayoyi na India, NBC suka kama ta, ta yi soyayya da Sushant Singh Rajput a watannin karshen rayuwansa.

An kama jaruma Rhea Chakbraborty kan laifin samar wa tsohon saurayinta jarumi Sushant Singh Rajput miyagun kwayoyi
An kama jaruma Rhea Chakbraborty kan laifin samar wa tsohon saurayinta jarumi Sushant Singh Rajput miyagun kwayoyi. Hoto daga LIB
Source: Twitter

Ana tuhumar jarumar da laifin yi wa marigayin jarumin na Bollywood safarar miyagun kwayoyi.

DUBA WANNAN: Garba Shehu: An sayar da man fetur N600 kowanne lita a mulkin PDP

NBC ta yi karar jarumar ne bayan an gano wasu sakonnin Whatsapp daga wayar Rhea Chakbraborty da ke nuna tana samar wa Sushant Singh Rajput kwayoyi a cewar jami'in hukumar NBC, Mutha Ashok Jain.

An kama jaruma Rhea Chakbraborty kan laifin samar wa tsohon saurayinta jarumi Sushant Singh Rajput miyagun kwayoyi
An kama jaruma Rhea Chakbraborty kan laifin samar wa tsohon saurayinta jarumi Sushant Singh Rajput miyagun kwayoyi. Hoto daga LIB
Source: Twitter

'Muna da hujojji akan Rhea hakan yasa muka kama ta. Babu bukatar mu cigaba da rike ta. Mun gamsu da tambayoyin da muka yi mata na kwanaki uku. Saboda mun riga mun yi wa wadanda muka kama tambayoyi.

Sai dai a wani jawabi mai ban mamaki da Rhea ta yi, ta ce kashi 80 cikin dari na jaruman Bollywood suna shan miyagun kwayoyi. Ta bayyana hakan ne a lokacin da NBC suka sada ta da alkali ta bidiyo.

NBC ta kuma shaidawa kotu cewa Rhea ta bayyana rawar da ta taka wurin samar wa Rajput kwayoyi da wasu harkokin kudi da suka yi da ya shafi wasu jarumai kamar Samuel Miranda, Dipesh Sawant da Showik Chakraborty.

KU KARANTA: Mun gaji da jan kafa da ka ke yi, ka canja shugabannin tsaro: Hadakar kungiyoyin arewa ga Buhari

Daga bisani an bata damar ta tafi kotu ta nemi beli. Akwai yiwuwar a yau Laraba za ta nemi belin.

An kama jaruma Rhea Chakbraborty kan laifin samar wa tsohon saurayinta jarumi Sushant Singh Rajput miyagun kwayoyi
An kama jaruma Rhea Chakbraborty kan laifin samar wa tsohon saurayinta jarumi Sushant Singh Rajput miyagun kwayoyi. Hoto daga LIB
Source: Twitter

Iyalan Rhea da lauyansu tunda farko sun ce suna tsamannin dama za a iya kama ta tun bayan kama dan uwan ta Showik a ranar Juma'a.

Mahaifin Rhea, Laftanat Kwanel Indirajit Chakbraborty ya yi jawabi a karshen makon da ta gabata kamar haka;

'Ina taya India murna, kun kama da na, ina kyautata zaton za ku kama 'ya ta itama daga nan kuma ban san wanda za ku sake kama wa ba.

A wani rahoton da Legit.ng ta wallafa, kun ji cewa wata amarya ta fice daga wurin daukar aure ta bazama a kan titi ta ce ta fasa auren.

Bidiyon amaryar ya nuna mutane da dama suna kokarin bata hakuri ta koma a daura auren amma hakan bai yi wu ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel