Karamar hukuma a Kaduna ta haramta almajiranci bayan almajirai 8 sun mutu a hatsarin jirgin ruwa

Karamar hukuma a Kaduna ta haramta almajiranci bayan almajirai 8 sun mutu a hatsarin jirgin ruwa

Shugaban ƙaramar hukumar Kubau a jihar Kaduna, Sabo Aminu Anchau ya ce an dakatar da almajiranci a ƙaramar hukumar biyo bayan hadarin jirgin ruwa da ya yi sanadin mutuwar almajirai 8 kamar yadda ya shaida wa Arewa Trust Weekly.

Arewa Trust Weekly ta ruwaito Gwamna Nasir El-Rufa'i a watan Afrilu ya soke almajiranci a jihar ya kuma bada umarnin a mayar da dukkan almajiran jihohin su na asali.

Anchau ya kuma ce an haramta dukkan wasu nau'ikan bautar da yara da cin zarafin su inda ya ƙara da cewa ba wai karatun Kur'ani bane aka hana sai dai cin zarafin yara da sunan karatun.

Karamar hukuma a Kaduna ta haramta almajiranci bayan almajirai 8 sun mutu a hatsarin jirgin ruwa
Karamar hukuma a Kaduna ta haramta almajiranci bayan almajirai 8 sun mutu a hatsarin jirgin ruwa. Hoto daga Djawa News
Source: Twitter

A "daminar bara karamar hukumar ta rasa almajirai guda takwas a rafin Gilmor.

"Malaminsu ya ɗauke su zuwa gonarsa ne da ke tsallaken rafi domin su masa aiki.

KU KARANTA: Boko Haram ta kashe mutum huɗu yayin da suke barci, ta ƙona wasu uku da ransu a Borno

"A hanyarsu ta dawowa, injin jirgin ruwan da suka shiga ya samu matsala a lokacin da jirgin ke tsakiyar rafi.

"Takwas cikin yaran sun daka tsalle sun fada cikin rafin a lokacin da ruwan ya fara ƙarfi kuma dukkansu sun mutu," in ji shi.

Ya nuna rashin amincewarsa da hakan inda yace wasu malaman suna amfani da almajirancin ne kawai domin bautar da yaran.

DUBA WANNAN: Bidiyo: Amarya ta fasa auren mijinta a lokacin da aka tafi wurin daurin aure

"Malaman makarantun almajirai babban ƙallubalai ne yunkurin da ƙaramar hukumar ke yi wurin samar da ilimi ga yara.

"Muna ƙokarin yin hadin gwiwa da gwamnatin jiha domin inganta harkar tare da tsaftace ta," in ji shi.

Shugaban ƙaramar hukumar ya ce sun samar da kujeru 650 don rabawa makarantu saboda dalibai su dena zama a ƙasa.

A wani labarin, kun ji cewa kwamishinan ƴan sanda na jihar Gombe, Shehu Maikudi a ranar Litinin ya gabatar wa manema labarai wasu masu safarar mutane huɗu da ƙananan yara 12.

Maikudi ya ce yan sanda sunyi nasarar kama yan kungiyar ne tare da hadin kai da taimakon iyayen yaran kamar yadda The Punch ta ruwaito.

A cewar Maikudi, wasu daga cikin iyayen sun shigar da rahoto cewa an sace yaransu. An kama daya daga cikin wadanda ake zargin a makon da ta gabata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel