Da duminsa: Sojoji sun hallaka kasurgumin dan bindigan jihar Benue, Terwase Gana

Da duminsa: Sojoji sun hallaka kasurgumin dan bindigan jihar Benue, Terwase Gana

Dubun Shahrarren dan bindigan da aka dade ana nema ruwa a jallo, Terwase Agwaza Gana, ya cika hannun jami'an Sojin 'Special forces' a jihar Benue, TVC ta ruwaito.

Kwamandan 4 Special Forces Command, Doma, jihar Nasarawa, Maj. -Gen. Moundhey Ali, ya bayyanawa manema labarai ranar Laraba cewa an kashe Gana ne a hanyar Gbese-Gboko-Makurdi bayan musayar wuta.

Yace, "Misalin karfe 12:00 na ranar Talata, mun samu labarin shahrarren dan bindiga Terwase Akwaza Agbadu wanda aka fi sani da Gana na hanyar Gbese-Gboko-Makurdi.

"Dakarun rundunar Operation ‘Ayem Akpatuma III’ suka bazama tare hanyar."

"Misalin karfe 13:00, an yi musayar wuta tsakanin Soji da Gana inda aka kasheshi."

Kwamandan ya ce an damke yaran aikinsa 40 da manyan makamai.

Ya ce yan bindigan na hannun Sojoji kuma za'a mikasu hannun yan sanda.

KARANTA WANNAN: Bayan amsan kudin fansa, yan bindiga sun kashe jami'in tsaro da dalibar makaranta a Kaduna

Da duminsa: Sojoji sun hallaka kasurgumin dan bindigan jihar Benue, Terwase Gana
Da duminsa: Sojoji sun hallaka kasurgumin dan bindigan jihar Benue, Terwase Gana
Source: UGC

Da dadewa an sanya kudi milyan goma ga duk wanda ya bayyana inda Gana yake boye a jihar amma ba'a samu wanda ya iya cin kudin ba.

Gabanin yanzu, ya mika kansa ga hukumar tare da ajiye makamai da harsasai ga mambobin kwamitin afuwa da gwamnan Jihar, Samuel Ortom, ya shirya.

Amma daga baya yayi hannun riga da gwamnatin Samuel Ortom lokacin da yake jam'iyyar All Progressive Congress bayan sabanin da suka samu.

Gana, wanda ake zargi da laifin kisan hadimin gwamna Ortom kan lamuran tsaro, Denen Igbana, ya koma mabuyarsa a daji.

Ana kyautata zaton cewa shine ummul haba'isin ayyukan yan bindiga a yankin Sankera da ya tattari Ukun, Logo da karamar hukumar Katsina Ala.

DUBA NAN: Sulhu alkhairi ne: Yan bindigan Sokoto sun mika wuya, su sake mutane 8 da suka sace

Matsalar rashin tsaro a Arewacin Najeriya ya zama abu daya da ya cigaba da zama babban kalubale ga al'ummar yankin.

Masu sharhi kan al'amuran yau da kullum na ganin cewa idan ba'a shawo kan lamuran tsaro ba harkokin tattalin arzikin yankin na iya durkushewa.

Bidiyon gawar:

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel