Dan wasan kwallon kafa a Najeriya ya fadi ya mutu a tsakiyar fili yayin da yake buga wasa
- Ana tsaka da wasan kwallon kafa a fili a jihar Osun wani dan wasa ya fadi a fili ya ce ga garinku nan
- Bayan faduwar shi dai an yi gaggawar garzayawa da shi zuwa asibiti domin ceto rayuwar shi
- Amma asibitin farko da suka fara zuwa sunki karbar shi, hakan ya sanya suka garzaya wani, kafin su karasa ya mutu
Dan wasan kwallon kafa na jihar Osun, da aka bayyana sunan shi da Damilola, ya fadi ya mutu, a daidai lokacin da yake buga kwallo a fili a yankin Ido dake jihar ta Osun.
A cewar wani wanda lamarin ya faru a kan idon shi, Damilola ya fadi a lokacin da yake bugawa kulob din shi na Premier Football Club Ofatedo, a ranar Litinin 7 ga watan Satumba, shekarar 2020, din nan da ta gabata.
Haka wakilin jaridar PUNCH ya gano cewa anyi gaggawar garzayawa da dan wasan zuwa asibiti domin yi masa magani a daidai lokacin da ya fadi a filin.
"Asibitin sun ki su karbe shi, hakan ya sanya aka garzaya da shi zuwa LAUTECH, inda a nan aka bayyana cewa ya mutu. A lokacin da ake buga zagaye na biyu a wasan, kawai sai ya fadi a tsakiyar fili ya kasa tashi.
"Bai taba nuna wata alama ta rashin lafiya ba. Dan wasa ne da a koda yaushe yake kokarin zuwa ya bugawa kulob din shi wasa," cewar wani abokin dan wasan, wanda ya bukaci jaridar ta PUNCH ta boye sunan shi.
KU KARANTA: Yakamata masu fadi a ji a Najeriya su yi mana adalci - Buhari
Ya kara da cewa, an binne marigayin a Ido Osun a jiya Talata 8 ga watan Satumba, 2020.
Babban jami'in kungiyar 'yan kwallon kafa na jihar Osun, Mr Leke Hamzat, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Haka kuma mun kawo muku rahoton wani yaro mai shekaru 11 mai suna PJ Brewer-Laye, ya zama jan gwarzo bayan da ya dauka matakin da kowanne mai hankali zai iya dauka wurin ceto rayuwar kakarsa mai suna Angela.
Kakarsa ta fara korafin jiri, rashin karfin jiki da kuma disashewar gani, amma babu wanda zai taimaka a gidan.
KU KARANTA: Karfin hali: Wani mutumi ya bindige matarshi har lahira a cikin ofishin 'yan sanda yayin da taje kai karar shi
Kamar yadda jaridar New York Post ta wallafa, a lokacin da tsohuwar ta fara jin jikinta babu dadi, ta fito inda ta jingina da wata alama da ke kan titi sannan jikanta da ke wasa ya hangota.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng