Bidiyo: Yaro mai shekaru 11 yayi ceton rai, ya tuka kakarsa a mota zuwa asibiti

Bidiyo: Yaro mai shekaru 11 yayi ceton rai, ya tuka kakarsa a mota zuwa asibiti

Wani yaro mai shekaru 11 kacal a duniya a yankin Indianapolis da ke Amurka ya bayyana bajintarsa bayan da ya ceci rayuwar kakarsa, inda ya tuka ta zuwa asibiti a motarsa kirar Mercedes Benz.

Yaron mai shekaru 11 mai suna PJ Brewer-Laye, ya zama jan gwarzo bayan da ya dauka matakin da kowanne mai hankali zai iya dauka wurin ceto rayuwar kakarsa mai suna Angela.

Kakarsa ta fara korafin jiri, rashin karfin jiki da kuma disashewar gani, amma babu wanda zai taimaka a gidan.

Kamar yadda jaridar New York Post ta wallafa, a lokacin da tsohuwar ta fara jin jikinta babu dadi, ta fito inda ta jingina da wata alama da ke kan titi sannan jikanta da ke wasa ya hangota.

"Ina jingine da wata alama a kan titi amma sai kawai ga jikana. Ina duban dama na hango motata kirar kamfanin Mercedes Benz tana tunkaro ni.

"A hankali ba tare da gudu ba take tunkaro ni. Daga lekawa na hango PJ a ciki," Angela ta tuna da hakan.

KU KARANTA: Gwamnan PDP ya tube rawanin sarkinsa, bayan ya ziyarci Buhari, ya maye gurbinsa

Dattijuwar ta jinjinawa PJ da yadda ya ja motar, inda tace ya yi tamkar kwararren direba wanda ya dade da koyon tuki.

"Shekarun yaron nan goma sha daya kacal amma yana tuki kamar kwararre. Bai taba daukar mota ba. Ya fi amfani da babur ko kuma kekensa. Muna fita a lokutan da nake son motsa jikina," tace.

Kakar tace jikanta wanda a yanzu yake girma kafin ya zama saurayi, ya kusan cika shekaru 12 amma kuma yana da tarin natsuwa da hankali.

"Ya tuka motar muka dawo gida. Ya hau kan titi kamar wani kwararren direba. Ya mayar da motar cikin gareji duk da kankantar shekarunsa," kakar tace.

Bidiyo: Yaro mai shekaru 11 yayi ceton rai, ya tuka kakarsa a mota zuwa asibiti
Bidiyo: Yaro mai shekaru 11 yayi ceton rai, ya tuka kakarsa a mota zuwa asibiti. Hoto daga The Nation
Source: Twitter

KU KARANTA: Hotuna: Mawaki Akon ya bayyana kudurinshi na gina birnin N2.3 tiriliyan wanda ya sakawa suna Akon City

A wani labari na daban, Yariman Dubai mai jiran Gado, Sheikh Hamdan bin Mohammed bin Rasha Al-Maktoum, ya nunawa duniya cewa ba komai bane idan ka zama mai adalci ga dabbobi.

Sheikh Mohammed ya dakata da amfani da motarsa mai kirar Mercedez Benz G-Wagon saboda ya samawa tsuntsayen guda biyu wajen da za suyi sheka. Yariman ya daina amfani da wannan mota domin ya tabbatar da lafiyar wadannan tsuntsaye.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel