'Yan bindiga sun kashe dan sanda 1, sun raunata wasu hudu

'Yan bindiga sun kashe dan sanda 1, sun raunata wasu hudu

Wasu 'yan daba 12 a ranar Litinin a yayin da ake ruwan sama sun kai wa 'yan sanda biyar hari a wata tashar mota da ke Okagwe a yankin Ohafia da ke jihar Abia.

Jami'an tsaro sun fake a tashar motar yayin da ake ruwan sama mai karfi a tashar mota da ke Okagwe a jihar Abia.

Kamar yadda kwamishinan yada labarai na jihar, John Okiyi Kalu, ya bayyana, ya ce wani sifetan dan sanda ya rasa ransa yayin da sauran hudun ke cikin wani mummunan hali.

Suna asibiti 'yan sandan jihar inda suke karbar taimakon gaggawa domin ceto rayukansu.

KU KARANTA: Babu kasar da ta kai Najeriya arhar man fetur a Afrika har yanzu - Lai Mohammed

Okiyi ya ce, "Gwamnatin jihar Abia tare da hadin guiwar jami'an tsaro a jihar a halin yanzu suna bincike a kan karanstaye da aka samu na tsaro.

"Lamarin ya auku a karamar hukumar Ohafia, wanda yayi sanadin mutuwar dan sanda daya tare da barin waus hudu a cikin mummunan halin rauni.

"Gwamnatin na kira ga jama'a da su garzaya ofishin 'yan sanda mafi kusa idan suka ga mutum da harbin bindiga.

Dukkan kokarin zantawa da kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Geoffrey Ogbonna, ya gagara.

'Yan bindiga sun kashe dan sanda 1, sun raunata wasu hudu
'Yan bindiga sun kashe dan sanda 1, sun raunata wasu hudu. Hoto daga The Punch
Asali: Twitter

KU KARANTA: Sau 1 nayi lalata da ita, ba sau 4 bane - Tsohon da yayi wa yarinya fyade

A wani labari na daban, Wani mutum mai suna Labaran Aliyu mai shekaru 33 a yankin Gidan Buhari da ke karamar hukumar Wamakko ta jihar Sokoto, ya shiga hannun hukuma a kan zarginsa da ake yi da damfarar wasu mutum 15 da suka hada da dan sanda.

Kwamandan hukumar Hisbah na jihar Sokoto, Dr. Adamu Bello Kasarawa, ya zargi wanda ake zargin da karbar kudi har naira miliyan 2.4 daga wurin wadanda ya damfarar da sunan zai buga musu kudi.

Kamar yadda hukumar Hisbah ta bayyana, wadanda ya damfarar ''yan jihohi daban-daban ne na sassan kasar nan.

"An kama wanda ake zargin bayan korafinsu sannan kuma an samu lambobin wayarsu a cikin wayar salularsa".

Ya ce dan sandan da aka damfara, amma an boye sunansa, a halin yanzu yana aikinsa a jihar Kaduna.

"Yana amfani da sihiri, yankan dabbobi, aljanu da duk wasu nau'in turaruka wurin yaudarar jama'a da damfara," Karasawa yace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel