N400,000 ake kashewa wajen jinyan kowani mai cutar Korona daya - El-Rufa'i

N400,000 ake kashewa wajen jinyan kowani mai cutar Korona daya - El-Rufa'i

- Gwamnan jihar Kaduna ya bayyana irin makudan kudin da yake kashewa wajen jinyan masu Korona

- El-Rufa'i ya bayyana hakan yayin ganawa da sarakunan gargagiyan Arewacin Najeriya

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya yi kira ga sarakunan Arewacin Najeriya kada suyi kasa a gwiwa wajen wayar da kan al'ummarsu kan hanyoyin kare kai daga cutar Korona.

Ya jaddada musu cewa su sani akwai matukar tsada jinyan wadanda suka kamu da cutar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a taron gangamin sarakunan Arewacin Najeriya karkashin jagorancin Sarkin Musulmi, Sa'ad Abubakar, a jihar Kaduna.

Ya fada musu cewa akan kashe kimanin N400,000 kan kowani mai cutar wajen jinya.

Ya ce ya zama wajibi mutane su kare kawunansu daga kamuwa da cutar saboda ba karamin illa cutar ke yiwa asusun jihohin Arewacin Najeriya ba.

Sarakunan jihohin Arewacin Najeriya 19 sun taru a jihar Kaduna ranar Litinin domin tattauna matsalan rashin tsaro da tattalin arzikin da ke kalubalantar yankin, Channels TV ta ruwaito.

N400,000 ake kashewa wajen jinyan kowani mai cutar Korona daya - El-Rufa'i
N400,000 ake kashewa wajen jinyan kowani mai cutar Korona daya - El-Rufa'i
Source: Twitter

DUBA NAN: Sulhu alkhairi ne: Yan bindigan Sokoto sun mika wuya

A jiya Sa’ad Abubakar III, Sultan na Sokoto, ya yi kira ga kawo karshen kashe-kashe a kudancin Kaduna.

Yankin ta fuskanci yawan hare-hare da ya yi sanadiyar rasa rayuka da dukiyoyi.

Da yake magana a taron kungiyar sarakunan arewa a Kaduna a ranar Litinin, 7 ga watan Satumba, basaraken ya bayyana rikicin a matsayin “hauka da ya zama dole a dakatar dashi cikin gaggawa”.

Ya yi kira ga wadanda ke da hannu a kashe-kashen da su daina mummunan aika-aikan, inda ya ce “hakan ya ishe su.”

Sultan ya ce: “babu wani mutum da ke cikin hankalinsa da zai je yana kashe-kashen bayin Allah bisa ko wani hujja.”

KU KARANTA KUMA: Sulhu alkhairi ne: Yan bindigan Sokoto sun mika wuya, su sake mutane 8 da suka sace

Basaraken ya kuma zargi yan siyasa da rura wutar rikicin, inda ya roki yan Najeriya da kada su bari a mayar da su karen farauta, jaridar The Cable ta ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Online view pixel