Sirikina ne yake son ganin bayan aurenmu - Matar aure ta sanar da kotu

Sirikina ne yake son ganin bayan aurenmu - Matar aure ta sanar da kotu

Wata mata mai suna Blessing Amuson a ranar Talata ta sanar da wata kotun gargajiya da ke zama a Ile-Tuntun a jihar Ibadan cewa ta tsinke aurensu mai shekaru uku.

Matar auren ta bukaci rabuwa da mijinta mai suna Babatunde sakamakon tsawwala mata da sirikinta yayi wanda tace yana kokarin lalata musu aure.

A yayin bayani a gaban alkali, Amuson , wacce ke zama a yankin Apata da ke Ibadan, ta ce: "Sirikina ne ke son kashe min aure da yadda yake gurbata tunanin mijina.

"Kafin aurena da Babatunde, na samu aiki mai kyau da gwamnatin jihar Legas kuma mun yi yarjejeniya cewa zan cigaba da aiki bayan aurenmu.

"Amma kuma, bayan auren ya canza kuma ya bukaci in ajiye aikina domin in dawo Ibadan.

"Sau da yawa, yana zuwa wurin iyayensa kuma a nan yake canza tunaninsa. Daga baya ya koreni daga gidansa.

“Wata rana, na dawo gida sai na ga ya sauya min makullin gida, hakan ya hana ni fita. Na kira shi amma sai yace mahaifinsa ne ya umarcesa da yayi hakan.

Sirikina ne yake son ganin bayan aurenmu - Matar aure ta sanar da kotu
Sirikina ne yake son ganin bayan aurenmu - Matar aure ta sanar da kotu. Hoto daga Daily Trust
Source: Twitter

KU KARANTA: FG ba za ta iya cigaba da kashe N5bn a kowanne wata ba a kan 'yan gudun hijira - Majalisa

“Iyayena sun kira shi fiye da a kirga amma ya ki daga wayarsu," Blessing tace.

Wanda ake karar ya samu wakilcin mahaifinsa, Johnson, ya kuma musanta zargin. Johnson ya ce dansa baya gari.

"Sirikata da iyayenta sune suke shirya komai. Mai shari'a, ban taba umartar da na ya rufe gidansa ba. Da na ba zai iya hakuri da miyagun halayyarta ba. Ta ki daukar ciki saboda tana hidimar kasa.

"Bata yadda ta zauna gidanta kuma mahaifiyarta tana goyon bayanta. Bata rayuwa kamar matar aure tun daga yadda take saka kaya. A hakan kuma mahaifinta malamin addinin kirista ne," yace.

A hukuncin alkalin kotun Henry Agbaje, ya umarci Babatunde da ya bayyana a zaman kotu na gaba. Ya basu shawarar su je su sasanta har zuwa ranar 21 ga watan Satumban 2020.

A wani labari na daban, bayanai sun nuna cewa a kalla mutum tara aka yanke wa hukuncin kisa a jihar Kano da ke yankin arewacin Najeriya daga farkon shekarar 2020 zuwa watan Augusta.

Kamar yadda takardun kotu daban-daban suka bayyana kuma BBC ta gani, an yanke wa mutanen hukuncin kisan bayan samunsu da aka yi da wasu manyan laifuka.

Bakwai daga cikinsu sun samu hukuncin kisan bayan da aka kama su da laifin kisan kai, daya daga ciki ya yi wa karamar yarinya fyade sai guda daya da yayi batanci ga Annabi Muhammadu (SAW).

KU KARANTA: Boko Haram: 'Yan ta'adda sun kashe mutum 10, sun yi garkuwa da manoma

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel