Karin kudin man fetur: 'Yan sanda sun ja kunnen mutanen dake shirin zanga-zanga a Borno

Karin kudin man fetur: 'Yan sanda sun ja kunnen mutanen dake shirin zanga-zanga a Borno

- An gargadi mutanen jihar Borno da suke shirin gabatar da zanga-zanga a jihar da su kuka da kansu

- Rundunar 'yan sandan jihar ce tayi wannan gargadi

- Rundunar tayi gargadin ne bayan samun labarin wasu kungiyoyi da suke shirin gabatar da zanga-zangar kan karin kudin wuta dana man fetur da gwamnatin tarayya tayi

Rundunar 'yan sandan jihar Borno ta gargadi mutane akan kowacce irin zanga-zanga dake zuciyarsu sakamakon karin kudin man fetur dana wutar lantarki da gwamnatin tarayya tayi.

A wata sanarwa da jami'in hulda da jama'a na hukumar 'yan sandan jihar Mr. Edet Okon ya fitar, ya ce har yanzu akwai dokar hana zanga-zanga a yankin na Arewa maso Gabas.

Karin kudin man fetur: 'Yan sanda sun ja kunnen mutanen dake shirin zanga-zanga a Borno
Karin kudin man fetur: 'Yan sanda sun ja kunnen mutanen dake shirin zanga-zanga a Borno
Source: Twitter

A cewar rundunar 'yan sandan, wannnan zanga-zanga za ta iya kawo matsala a zaman lafiyar da aka shafe tsawon lokaci kafin a kawo jihar.

Sanarwar ta ce:

"Rundunar 'yan sandan jihar Borno ta gano cewa akwai shirin da wasu kungiyoyi suke yi na kawo karshen wannan zaman lafiya da muka shafe tsawon lokaci kafin mu samu a jihar nan ta hanyar gabatar da zanga-zanga, saboda karin kudin man fetur dana wutar lantarki da kuma tsarin ma'aikatan gwamnati da ma'aikatan N-Power.

KU KARANTA: Karfin hali: Wani mutumi ya bindige matarshi har lahira a cikin ofishin 'yan sanda yayin da taje kai karar shi

"Saboda haka ne, kwamishinan 'yan sanda na jihar Borno, CP Mohammed Ndatsu Aliyu, yayi gargadin cewa rundunar ba za ta amince da gabatar da irin wannan zanga-zanga ba, saboda irin wannan zanga-zanga za ta kawo matsala a zaman lafiyan da jami'an tsaro suka shafe tsawon lokaci ana nema a jihar, hakan ya sanya tayi alkawarin ganin ta tabbatar da zaman lafiya a jihar.

"Rundunar tana amfani da wannan dama ga al'umma cewa an haramta zanga-zanga kowanne iri ne a tsakanin al'umma a jihar nan.

"Rundunar ta roki al'umma da suyi hakuri su zauna lafiya domin cigaban kowa da kowa na jihar.

"Ana bukatar duk masu shirin yin zanga-zanga da su cire wannan niyyar su kuma bi dokokin da aka gindaya a jihar nan."

KU KARANTA: Bidiyo: Yariman Dubai ya ajiyewa tsuntsaye wata sabuwar mota ta alfarma da za su dinga shakatawa a ciki

Idan ba a manta ba Legit.ng ta kawo muku rahoton yadda Shehun Borno ya bayyana cewa 'yan Boko Haram sun kashe mishi Hakimai da Dagatai da yawan gaske a masarautar shi.

Shehun Borno, Alhaji Garbai El-Kanemi, ya bayyana cewa an kashe Hakimai 13 da kuma Dagatai da yawan gaske a cikin Masarautarsa, a lokacin da Boko Haram ke cin karenta babu babbaka.

Sarkin ya bayyana haka ne a Maiduguri a wata ziyara da tawagar Sanatoci suka kawo masa, wacce Sanata Abubakar Yusuf, yake jagoranta, domin ganin yanayin aikin da Kwamitin Cigaban Arewa maso Gabas (NEDC) take yi a yankin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel