Hadi Sirika: Sau 10 ana yi mani gwajin COVID-19, ana kuma ganin ban kamu ba

Hadi Sirika: Sau 10 ana yi mani gwajin COVID-19, ana kuma ganin ban kamu ba

- Hadi Sirika ya bayyana yadda ya yi dace, COVID-19 ta buga ta bar shi

- Ministan harkokin jiragen saman ya ce sau 10 ya na gwajin COVID-19

- Sanata Sirika ya yi sa’a har yanzu bai kamu da cutar Coronavirus ba

Ministan harkokin jiragen saman Najeriya, Hadi Sirika ya bayyana yadda ya sha gwaje-gwaje domin ya gano ko ya na dauke da kwayar cutar COVID-19.

Mai girma Ministan ya ce ya yi ta yin gwajin COVID-19, kuma duk lokacin da sakamako ya fito, sai ya ga cewa wannan mummunar cuta ba ta harbe shi ba.

Hadi Sirika ya ce daga lokacin da aka fara fama da annobar COVID-19 zuwa yanzu ya yi gwajin Coronavirus sau goma, amma ya yi dace cutar ba ta harbe shi ba.

Sanata Hadi Sirika ya bayyana wannan ne a shafinsa na Twitter a ranar 6 ga watan Satumba, 2020.

KU KARANTA: COVID-19: Gwamnan Bauchi ya yi na'am da aiki da 'chloroquine'

Hukumar NCDC ta bayyana cewa ta yi wa mutane kusan 300, 000 gwajin COVID-19 a Najeriya. Sai an yi wannan gwaji ne ake iya tabbatar da halin lafiyar mutum.

Ministan ya godewa Ubangiji da ya ba shi damar tsallakewa tarkon wannan cuta ta murar mashako. Hadi Sirika ya yi wa wadanda su ka kamu addu’ar samun lafiya.

A karshen jawabinsa, tsohon Sanatan na arewacin jihar Katsina ya roki Ubangiji ya kawowa al’umma karshen wannan cuta domin Duniya ta samu sauki.

Ga cikakken abin da Sirika ya rubuta a ranar Lahadi:

KU KARANTA: Za ayi fama da karancin abinci a Garuruwa saboda COVID-19 - NBS

Hadi Sirika: Sau 10 ana yi mana gwajin COVID-19, ana kuma ganin ban kamu ba
Ministan harkokin jirage, Hadi Sirika Hoto: Reuters
Asali: Facebook

“Daga lokacin da aka fara COVID-19, an yi mani gwaji sau tara, duk ana samun cewa ba na dauke da kwayar cutar.”

Ya kara da cewa: “Kwanakin baya aka dauki jinina, aka yi mani gwaji na goma, shi ma ya nuna cewa cutar ba ta harbe ni ba.”

“Dukkan godiya ta tabbata ga Allah. Ina yi wa wadanda su ka kamu fatan samun waraka cikin gaggawa.” inji Ministan.

A karshe Sirika ya rubuta: "Allah ya kawo mana karshensa ba da dadewa ba. Allah ya ceci al’umma.”

Idan ba ku manta ba a cikin ministocin tarayya, ministan harkokin kasar waje ne kawai ya kamu da cutar, kuma ya samu lafiya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel