NBS: Akwai matsalar rashin isasshen abinci a Legas, Kano, Ribas, da Abuja

NBS: Akwai matsalar rashin isasshen abinci a Legas, Kano, Ribas, da Abuja

Annobar COVID-19 da ta barke ta jawo karin karancin abinci a wasu wurare. Hukumar NBS mai tara alkaluma a kasa ta bayyana wannan.

Rahoton NBS ya bayyana cewa wannan annoba ta Coronavirus ta jawo barazanar rashin isasshen abinci a Kano, Legas, Ribas da babban birnin tarayya.

A rahoton da NBS ta fitar a ranar Litinin, an gano cewa ana fama da rashin isasshen abinci a wadannan garururuwa, musamman Ribas da Abuja.

A Ribas da birnin tarayya Abuja, da-dama na mutanen garuruwan su na hakura da cin abinci sau daya tun da COVID-19 ta barke a kasar kwanakin baya.

KU KARANTA: Annobar COVID-19 za ta iya jawo cututtuka masu hadari ga yara

Ga abin da rahoton ya ce:

“Karancin kayan abinci ya yi kamari a jihohin nan hudu, musamman Ribas da Abuja inda 79% da 72% na mutanen jihohin su ka yafe cin abinci sau daya daga shigowar COVID-19.”

“Gidaje a duk jihohin nan hudu su na ciro kudin da su ka ajiye a asusu ko ma su ci bashi domin dawainiyar rayuwarsu ta yau da kullum.”

NBS ta ce wannan halin da aka shiga ciki zai jefa al’umma cikin hadarin tattalin arziki ta yadda ba za su samu ikon yi wa kansu abubuwan jin dadi ba.

KU KARANTA: NCDC ta fitar da sababbin alkalumar masu COVID-19 a jiya

NBS: Akwai matsalar rashin isasshen abinci a Legas, Kano, Ribas, da Abuja
Shugaban NBS, Dr. Yemi Kale Hoto: Punch
Asali: Twitter

Rahoton ya kuma nuna yadda ayyukan da mutane su ke yi yayi kasa a jihohin nan hudu, idan aka kamanta da halin da ake ciki kafin COVID-19 ta shigo Najeriya.

An samu raguwar kashi 14% na masu fita aiki a babban birnin tarayya Abuja a daidai wannan lokaci. A irinsu Abuja da Legas, babu yawan manoma kamar sauran jihohin.

“Ko da an dawo aiki, kudin da ke shiga aljihun mutane zai rika rawa, ganin mafi yawan mutanen da ke noma su na Kano da Ribas, da wasu tsiraru a Legas kafin COVID-19.”

A lokacin da ake kukan halin matsanancin tattalin arzikin da ake ciki, kun ji gwamnatin tarayya ta kara farashin kudin wutar lantarki da litar man fetur a watan Satumban nan.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel