Karfin hali: Wani mutumi ya bindige matarshi har lahira a cikin ofishin 'yan sanda yayin da taje kai karar shi

Karfin hali: Wani mutumi ya bindige matarshi har lahira a cikin ofishin 'yan sanda yayin da taje kai karar shi

- Mijin da matarshi ta je ofishin 'yan sanda domin kai karar shi akan abubuwan da yake yi mata

- Ya bita har cikin ofishin 'yan sandan ya harbeta da bindiga a gaban jami'an 'yan sanda

- Sai dai kuma an samu nasarar kama shi kuma an samu nasarar kwace bindigar daga hannun shi

Wani irin lamari mai cike da tashin hankali ya faru a ofishin 'yan sanda na Madeira dake Mthatha, cikin kasarAfrika ta Kudu, yayin da wani mutumi ya harbe matar shi mai shekaru 28, a cikin ofishin 'yan sandan a lokacin da taje kai karar shi.

Mutumin wanda aka bayyana cewa yana aikin gadi ne a wani kamfani, an kama shi a cikin ofishin 'yan sandan, bayan ya karar da harsashin cikin bindigar akan matar.

Karfin hali: Wani mutumi ya bindige matarshi har lahira a cikin ofishin 'yan sanda yayin da taje kai karar shi
Karfin hali: Wani mutumi ya bindige matarshi har lahira a cikin ofishin 'yan sanda yayin da taje kai karar shi
Asali: Facebook

Wasu shaidu da lamarin ya faru a gabansu lokacin da suke ofishin 'yan sandan, sun ranta ana kare a kokarin da suke na tsira da rayukansu.

Wani da lamarin ya faru a gabanshi mai suna, Songezo Sanazo ya bayyanawa jaridar Dispatch Live cewa:

"Ina wajen ina kokarin karbar wasu takardu kawai sai naji harbin bindiga.

"Na jiyo na farko, na dauka ba komai bane. Amma sai na gudu na boye a jikin bango a lokacin dana jiyo tashin bindigar a karo na biyu, na uku dana hudu ya sanya mutane suka fara gudun tsira da rayukansu suna ihun neman taimako. Dukkan mu hankulan mu sun tashi matuka."

KU KARANTA: Ciki 15 na zubar saboda mijina, yanzu kuma yana son sakina - Matar aure ga kotu

Kakakin rundunar 'yan sandan, Birigediya Tembinkosi Kinana wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce mutumin ya yi kokarin guduwa kafin a samu nasarar cafke shi, bayan yayi harbin a ranar Litinin 7 ga watan Satumba.

Ya ce:

"A lokacin da ta shigo take sanar da jami'in dan sanda halin da take ciki. mijin ya shigo ofishin ba tare da yace komai ba ya fara harbin matar, wacce ta ji ciwuka da dama a wajen.

"An samu nasarar kwace bindigar da ya shiga wajen da ita, inda kuma za a gabatar da bincike a kan shi."

Kinana ya ce mai laifin zai bayyana a gaban kotu bisa zargin shi da ake yi da aikata kisan kai da zarar sun kammala bincike akan wannan lamari mai ban tsoro da.

KU KARANTA: Yadda malami ya ja dalibarsa bandaki, ya nemi yin lalata da ita

A wani rahoto makamancin haka, Legit.ng ta kawo muku rahoton yadda wani Anthony Edijala mai shekaru 39 ya shiga hannun 'yan sanda bayan muguwar aika-aikar da yayi wa budurwarsa, kuma mahaifiyar 'ya'yansa biyu.

Saurayin nata ya sassarata da gatari bayan da suka samu matsala a kan zarginta da yayi da amfani da asiri wurin tsotse masa mazakuta.

Wani dan uwan budurwar mai suna Felix Broma, ya bayyana cewa an kwashi 'yar uwarsa rai a hannun Allah zuwa babban asibitin Ughelli, inda take samun taimakon likitoci.

Ya tabbatar da cewa, yana tsoron shanyewar bangaren jiki ga 'yar uwarsa sakamakon jerin ayyukan da aka mata.

Ganau ba jiyau da suka ga yadda lamarin ya auku, sun sanar da Vanguard cewa sai da 'yan sanda suka zo wurin sannan suka samu damar karbar saurayin daga hannun jama'ar da suka nada masa mugun duka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel