Bidiyo: Yariman Dubai ya ajiyewa tsuntsaye wata sabuwar mota ta alfarma da za su dinga shakatawa a ciki

Bidiyo: Yariman Dubai ya ajiyewa tsuntsaye wata sabuwar mota ta alfarma da za su dinga shakatawa a ciki

- Yariman Dubai mai jiran Gado, Sheikh Hamdan bin Mohammed bin Rashid Al-Maktoum, ya daina amfani da wata hadaddiyar motar shi ta alfarma mai kirar Mercedes Benz g Wagon don tabbatar da lafiyar wasu tsuntsaye

- A wani bidiyo da yake ta yawo a shafukan sadarwa, an gano tsuntsayen sun yi sheka kuma sun yi kwai a ciki

- Dalilin da ya sanya Sheikh Mohammed yayi hakan shine domin ya tabbatar da cewa tsuntsayen da kwayayensu sun zauna lafiya

Yariman Dubai mai jiran Gado, Sheikh Hamdan bin Mohammed bin Rasha Al-Maktoum, ya nunawa duniya cewa ba komai bane idan ka zama mai adalci ga dabbobi.

Sheikh Mohammed ya dakata da amfani da motarsa mai kirar Mercedez Benz G-Wagon saboda ya samawa tsuntsayen guda biyu wajen da za suyi sheka.

Yariman ya daina amfani da wannan mota domin ya tabbatar da lafiyar wadannan tsuntsaye.

A wani bidiyo da yake ta yawo a shafukan sadarwa, an gano tsuntsayen guda biyu suna shirin zama iyaye, inda aka gansu suna yin sheka a cikin motar.

Bidiyo: Yariman Dubai ya ajiyewa tsuntsaye wata sabuwar mota ta alfarma da za su dinga shakatawa a ciki
Bidiyo: Yariman Dubai ya ajiyewa tsuntsaye wata sabuwar mota ta alfarma da za su dinga shakatawa a ciki
Asali: UGC

Haka kuma bidiyon ya nuna yadda tsuntsayen suka yi kwai a cikin wannan hadaddiyar mota ta alfarma.

Haka kuma an zagaye motar da wani jan abu duka domin tabbatar da cewa babu abinda ya samu tsuntsayen a lokacin da suke yin shekar su.

KU KARANTA: Dole ne a sake zabar Donald Trump idan har ana son zaman lafiya a Amurka - Cewar 'yar Uwar Osama bin Laden

KU KARANTA: An yankewa wani mutumi hukuncin kisa bayan an tsinci gawarwakin wasu mata guda biyu a cikin firjin shi

Haka kuma, Legit.ng ta kawo muku rahoton wani bidiyo na Yariman Dubai din lokacin da yake kiran rakuman shi da sunaye daban-daban.

A bidiyon da shi Yariman ya wallafa da kanshi a shafinsa na Instagram, an jiyo Yariman yana kiran rakuman nashi guda biyu da sunayen Fares, da Emaar.

Da farko dai Fares ne kawai ya fara amsawa, inda ya sanyo kanshi cikin kofar motar shi, Sheikh Hamdan ya bukaci rakumin ya kirawo Emaar, ai kuwa sai ya juya ya tafi ya kirawo ta.

A lokacin da Fares ya dawo wajen motar tare da Emaar, Sheikh Hamdan ya ce: "Emaar zo nan, zo nan."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel