Cigaba: Ganduje ya saka na'urorin sa-ido a manyan titunan Kano, bidiyon yadda suke aiki

Cigaba: Ganduje ya saka na'urorin sa-ido a manyan titunan Kano, bidiyon yadda suke aiki

Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya kammala saka na'urorin sa-ido a kan wasu daga cikin manyan titunan birnin Kano domin inganta tsaro da saukakawa jami'an tsaro aiki.

A wani takaitaccen sako da Salihu Tanko Yakasai, hadimin Ganduje, ya wallafa a shafinsa na tuwita, an nuna bidiyon yadda jami'an 'yan sanda ke kallon motsin mutane da ababen hawa a manyan titunan.

"Duk da Kano tana cikin jihohin da ke da zaman lafiya a Najeriya a shekaru 5 da suka gabata, mai girma gwamna Abdullahi Umar Ganduje bai daina kokarin kara karfafa tsaro a jihar Kano ba, saboda gwamnatinsa ta saka na'urorin sa-ido a manyan titunan birnin Kano.

"Ana sarrafa na'urorin daga dakin na musamman a hedikwatar 'yan sandan Kano," kamar yadda Yakasai ya bayyana.

Ko a kwanakin baya gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da cewa ta saka irin wadannan na'urori a cikin birnin Kaduna domin inganta tsaro.

Jama'a da dama da suka yi magana a kan sakon da Yakasai ya wallafa, sun yabawa kokarin gwamna Ganduje na zamanantar da tsaro a Kano.

Cigaba: Ganduje ya saka na'urorin sa-ido a manyan titunan Kano, bidiyon yadda suke aiki
Ganduje
Source: UGC

Wasu daga cikinsu sun yi kira da sauran gwamnonin jihohin arewa su yi koyi da irin wannan cigaba da Ganduje ya kawowa Kano, a cewarsu, hakan zai taimaka wajen saurin gano batagari da kuma daukan mataki a kan lokaci.

KARANTA: Buhari zai kaddamar da shirin tallafawa 'yan kasuwa da N50,000 a kowanne wata

KARANTA: Bikin Hanan: 'Ba kai mana adalci ba' - Aisha Buhari ta koka a kan wanda ya yi zanen barkwanci

A daren ranar Lahadi ne hedikwatar rundunar tsaro ta kasa (DHQ) ta sanar da cewa ta tsaurara matakan tsaro a Abuja da wasu makwabtan jihohi bayan samun labarin cewa kungiyar Boko Haram tana shirin kai wasu hare-hare.

DHQ ta ce ta gaggauta daukan wannan mataki ne bayan hukumar kwastam ta Najeriya (NCS) ta fitar da wata sanarwa domin ankarar da mazauna Abuja da wasu makwabtan jihohi a kan shirin kai hare-haren.

Manjo Janar John Enenche, kakakin DHQ, ya ce rundunar soji ta sanar da dukkan dakarunta su kasance cikin shirin 'ko ta kwana'.

A cikin wata sanarwa da hukumar Kwastam ta fitar, ta ce mayakan kungiyar Boko Haram suna shirin kaddamar da wasu hare-hare a Abuja, jihar Kogi da kuma jihar Nasarawa.

Sai dai, a cikin jawabin da Enenche ya fitar ranar Lahadi, DHQ ta bayyana cewa za ta yi kokarin dakile kai hare-haren.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel