Saurayi ya sassara budurwarsa a kan zarginta da asirin tsotse masa mazakuta

Saurayi ya sassara budurwarsa a kan zarginta da asirin tsotse masa mazakuta

Wata mahaifiyar yara biyu da ke cikin shekarunta na 30 na kokarin ganin yadda za ta tashi muguwar jinyar da ta fada bayan rikicin da tayi da saurayinta kuma uban 'ya'yanta.

Saurayin nata ya sassarata da gatari bayan da suka samu matsala a kan zarginta da yayi da amfani da asiri wurin tsotse masa mazakuta.

Budurwar da ke fama da jinya mai suna Augsutina Jowho Broma, tana fama da sarar da saurayin nata yayi mata a kai da kashin baya.

Anthony Edijala mai shekaru 39 ya shiga hannun 'yan sanda bayan muguwar aika-aikar da yayi wa budurwarsa, kuma mahaifiyar 'ya'yansa biyu.

Wani dan uwan budurwar mai suna Felix Broma, ya bayyana cewa an kwashi 'yar uwarsa rai a hannun Allah zuwa babban asibitin Ughelli, inda take samun taimakon likitoci.

Ya tabbatar da cewa, yana tsoron shanyewar bangaren jiki ga 'yar uwarsa sakamakon jerin ayyukan da aka mata.

Ganau ba jiyau da suka ga yadda lamarin ya auku, sun sanar da Vanguard cewa sai da 'yan sanda suka zo wurin sannan suka samu damar karbar saurayin daga hannun jama'ar da suka nada masa mugun duka.

Saurayi ya sassara budurwarsa a kan zarginta da asirin tsotse masa mazakuta
Saurayi ya sassara budurwarsa a kan zarginta da asirin tsotse masa mazakuta. Hoto daga Vanguard
Source: Twitter

KU KARANTA: Tirkashi: Rikici ya hado saurayi da budurwa ta dauki wuka ta caka masa yace ga garinku nan

A yayin tabbatar da aukuwar lamarin ga jaridar Vanguard, majiya daga jami'an tsaro ta ce wanda ake zargin ya amsa laifinsa, kuma ya ce sun yi fada da budurwar tasa wanda hakan yasa kowa ya kama hanyarsa.

Amma kuma daga bisani, ya gane cewa laifinsa ne a dukkan fadan da suka yi.

Majiyar da ta bukaci a boye sunanta, ta ce, "Yana zargin budurwarsa da yin asirin da ya tsotse mazakutarsa wacce yace a baya ta fi hakan girma. Hakan ne yasa suka yi baran-baran.

"A ranar da lamarin ya faru, ya je shagon da take saide-saide domin ganin 'ya'yan da suka haifa. Atake rikici ya barke inda budurwar ta fito da gatari domin kare kanta.

"Babu kakkautawa wanda ake zargin ya karba gatarin tare da sassara mata a kai da kashin baya."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel