Bikin Hanan: 'Ba kai mana adalci ba' - Aisha Buhari ta koka a kan wanda ya yi zanen barkwanci
Aisha Buhari, uwargidan shugaban kasa kuma uwar amarya, Hanan Buhari, ta yi korafi da mai zanen barkwanci, Mustapha Bulama.
A karshen makon jiya ne aka sha bikin auren Hanan, autar shugaban kasa, Muhammadu Buhari, da angonta, Turad Sha'aban, hadimi wurin minsitan aiyuka da gidaje, Babatunde Fashola.
Hotunan bikin Hanan da Turad sun mamaye kafafen sadarwa da dandalin sada zumunta har ma sun zama abun tattaunawa a tsakanin 'yan Najeriya.
Ganin cece-kucen da hotunan suka haifar ne yasa Bulama ya yi wani zanen barkwanci a kan bikin Hanan.
A hoton barkwanci da Bulama ya zana kuma jaridar Daily Trust ta wallafa, an nuna 'yan Najeriya suna kallon hotunan bikin Hanan a yayin da ake shagalin biki a can inda basu da ikon zuwa; wato sama ta yiwa yaro nisa.
Sai dai, barkwancin da Bulama ya yi bai yi wa Aisha Buhari dadi ba, lamarin da yasa ta bayyana cewa 'bai yi wa bikin 'yarta adalci ba'.
Aliyu Abdullahi, kakakin Aisha Buhari, ya shaidawa BBC Hausa cewa 'ya'yan shugaban kasa nada ikon yin aure idan lokacinsu ya yi.
KARANTA: Matsin rayuwa: Yadda hotunan kanin gwamna yana aswaki da naman kaji ya haifar da cece-kuce
KARANTA: Hotuna: Mawaki Dauda Kahutu Rarara ya gwangwaje Bashir Maishadda da sabuwar mota
Ya kara da cewa auren Hanan bashi da alaka da halin da 'yan kasa ke ciki na walwala ko sabanin hakan.
Abdullahi ya bayyana cewa tun saura wata guda kafin bikin Aisha Buhari ta gargadi hadimanta cewa ba za ai shagalin biki ba.
Kazalika, ya bayyana cewa dukkan hotunan ma'auratan da Aisha Buhari ta wallafa an yisu ne bayan biki.
"Kwata-kwata babu wani armashi, haka aka yi bikin sulu, na tabbatar da hakan."
"Babu adalci a cikin hotunan barkwanci da Bulama ya zana. Babu wata alaka a tsakanin bikin diyar shugaban kasa da yanayi ko halin da jama'a suka tsinci kansu," a cewar kakakin.
Dangane da bidiyon ruwan kudi da aka ga ana yi wa Amarya da Ango lokacin biki, Abdullahi ya ce babu ruwan Aisha Buhari ko fadar shugaban kasa.
"Wannan bidiyo ma ba a Abuja ba ne, a gidansu Ango ne a Kaduna. Su ne suke likin kudi bayan an kai amarya," a cewarsa.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng