Gwamnan PDP ya tube rawanin sarkinsa, bayan ya ziyarci Buhari, ya maye gurbinsa

Gwamnan PDP ya tube rawanin sarkinsa, bayan ya ziyarci Buhari, ya maye gurbinsa

Daya daga cikin dakatattun sarakunan gargajiya na jihar Anambra, Igwe Alex Edozieuno na Mkpunando Aguleri na karamar hukumar Anambra ta gabas, ya rasa rawaninsa.

An dakatar da basaraken tun farko bayan da ya kaiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari ziyara. An maye gurbinsa da Igwe Johnson Onyeaka - Mbanefo

An yi nadin sabon basaraken a filin Ukwuana - Isokwe da ke Mkpunando Aguleri inda aka sha shagali. Mata, kananan yara, matasa da dattawa duk sun samu halartar nadin sarautar.

An gano cewa, yankin yana da sassa hudu wadanda suka hada da Ugwuoba, Umuagu na Obeke, Ivite Enu da Igboezunu. Dukkan yankunan sun amince da nadin sabon sarkin.

Mutumin da yafi kowa tsufa a yankin, Iche Melionwu Udalor, ya nuna jin dadinsa a kan yadda suka samu sabon shugaba kuma zabin Ubangiji. Ya yi fatan sabon basaraken zai samu baiwar hikima daga magabata ta yadda zai yi zamaninsa.

A yayin nadin sarautar, Ichie Augustin Akwobi, wanda shine shugaban sarakunan gargajiyar yankin, ya ce ganin yadda tsohon basaraken ya yi rashin biyayya ga gwamnati, babu shakka magabantansu da suka mutu suna fushi da shi.

Gwamnan PDP ya tube rawanin sarkinsa, bayan ya ziyarci Buhari, ya maye gurbinsa
Gwamnan PDP ya tube rawanin sarkinsa, bayan ya ziyarci Buhari, ya maye gurbinsa. Hoto daga Vanguard
Asali: Depositphotos

KU KURANTA: Tirkashi: Rikici ya hado saurayi da budurwa ta dauki wuka ta caka masa yace ga garinku nan

Kuma tabbas dukkan yankin Mkpunando sun fusata, hakan ya kawo hukuncinsu na amincewa da zaben Onyeaka Mbanefo, wanda suke ganin ya matukar cancanta.

A yayin godiya ga dukkan jama'ar yankin da suka amince da shi, Igwe Onyeaka-Mbanefo, ya dauka alkwarin cewa ba zai basu kunya ba, Vanguard ta wallafa.

Ya ce duk abinda jama'ar yankin suke so shi za a yi tunda sune suka bukaci ya hau karagar sarautarsu. Ya kara da addau'ar samun nasara tare da tsawon rai ga mabiyansa.

Basaraken tare da wasu dattawan yankin, masu sarauta da sauransu sun kwashi rawa inda suka zagaye kauyukan yankin.

Legit.ng ta ruwaito cewa, rikicin shugabanci da iko tsakanin Gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano da masu sarautar garagjiya na jihar yana kara kamari.

Obiano ya dakatar da masu sarautar gargajiya 12 a jihar sakamakon ziyarar da suka kai wa shugaban kasa Muhammadu Buhari a makon da ya gabata.

Ya dakatar da wani basarake mai suna Igwe Peter Uyanwa, a kan zarginsa da yake da kai korafi daga yankinsa. Ya kara da janye shaidar amincewa ta basaraken.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel