Da duminsa: 'Yan daba sun zagaye majalisar jihar Ondo

Da duminsa: 'Yan daba sun zagaye majalisar jihar Ondo

Wasu 'yan daban siyasa a ranar Litinin da safe sun zagaye majalisar jihar Ondo, lamarin da ya kawo tsoro a zukatan jama'a, jaridar The Punch ta wallafa.

An ga 'yan daban da zasu kai a kalla 100 a babbar kofar shiga ginin majalisar, tare da wasu ababen hawa da suka ajiye a titin da zai kai mutum babban ginin majalisar.

An gano cewa, ganin 'yan daban ba zai rasa alaka da rikicin da ke tsakanin wasu daga cikin 'yan majalisar ba.

An gano cewa 'yan daban sun je wurin domin wasu 'yan majalisar ne da suke jira su fito.

Amma kuma, jami'an 'yan sandan da ke ginin majalisar sun hana 'yan daban shiga ciki.

Jami'an tsaron sun saka shinge a hanyar shiga majalisar, sannan suna tantance duk wanda zai shiga ginin majalisar.

Karin bayani na nan tafe...

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel