Dalilin da ya hana Mamman Daura halartar shagalin bikin Hanan Buhari

Dalilin da ya hana Mamman Daura halartar shagalin bikin Hanan Buhari

Duk da bayyana Mamman Daura da aka yi a matsayin uban taron auren Hanan Buhari da Muhammad Turad, dan uwan shugaban kasar kuma shakikinsa bai samu halartar taron bikin ba.

SaharaReporters ta wallafa cewa, rashin halartar Mamman Dauran ba ya rasa alaka da tafiyar da yayi zuwa Dubai domin a duba lafiyarsa sakamakon rashin lafiyar da yake fama da ita.

Idan za mu tuna, Mamman Daura ya yi tafiya zuwa Ingila tun a cikin watan Augustan da ta gabata. An fara rade-radin rashin lafiyarsa, amma wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta ya karyata hakan.

A bidiyon, an ga Mamman Daura na waya da shugaba Buhari a yayin da yake hutawarsa a wani masauki da ke Ingila.

Tsohon dan jaridar na daga cikin wadanda ake zargi na da kusanci da shugaban kasa Buhari, kuma suna amfani da hakan wurin juya akalar mulkin kasar nan.

Tuni dai an gano cewa Mamman Daura na da ciwon koda, wanda hakan yasa yake ziyartar kasahen Turai domin duba lafiyarsa.

Wata majiya wacce ta tabbatar da rashin halartarsa bikin, ta ce an yi shagalin bikin a babban dakin taron da ke kallon ofishin shugaban kasa, a maimakon dakin taro na banquet inda aka saba saukar manyan sha'anoni.

Majiyar ta sake jaddada cewa, mutum 80 kacal suka halarci taron bikin saboda jaddada kiyaye dokokin dakile yaduwar muguwar cutar korona.

Har yanzu kuwa rashin halartar Daura bikin ya janyo cece-kuce a cikin 'yan siyasa, ballantana makusantan shugaba Buhari.

Dalilin da ya hana Mamman Daura halartar shagalin bikin Hanan Buhari
Dalilin da ya hana Mamman Daura halartar shagalin bikin Hanan Buhari. Hoto daga Daily Trust
Asali: UGC

KU KARANTA: Kaduna: 'Yan bindiga sun kai hari Kajuru, mutum 2 sun rasu, an yi awon gaba da 5

A wani labari na daban, bidiyon yadda ake ruwan kudi a bikin diyar shugaban kasar Najeriya, Hanan Buhari da Turad Sha'aban, ya janyo cece-kuce a kafafen sada zumuntar zamani.

Wannan bidiyon ya bayyana ne bayan a kalla watanni biyu da bidiyon dan antoni janar kuma ministan shari'a, Abdulazeez Malami, ya bayyana inda ya yi aure kuma aka dinga watsi da Naira a jihar Kebbi.

A bidiyon, an ga angon da amarya tare da jama'a da yawa sun watsa musu kudi. Duk da ba sabon abu bane mannawa mutum kudi a biki, babban bankin Najeriya ya hana wannan lamari a sashi na 21 na dokokinsa na 2007.

Hakan zai iya sa a ci tarar mutum N50,000 ko daurin watanni shida a gidan maza A saboda wannan dokar ta babban bankin Najeriya, 'yan sanda sun saba kama jama'a da ke siyar da sabbin kudade a wuraren bukukuwa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel