Dalilin da yasa gwamnatin tarayya ta cire tallafin man fetur - Fadar shugaban kasa

Dalilin da yasa gwamnatin tarayya ta cire tallafin man fetur - Fadar shugaban kasa

Malam Garba Shehu, babban mai bai wa shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari, shawara a fannin yada labarai, ya ce gwamnatocin da suka shude basu da karfin guiwar daukar matakan da suka dace.

A wata takardar da Shehu ya fitar a ranar Lahadi, ya ce za a tuna da shugaban kasa Muhammad Buhari ko nan gaba, a matsayin shugaban da ya bada "gudumawa ga habakar tattalin arziki da ci gaban kasar nan, tare da kawo karshen dukkan wata rashawa da ke tattare da tallafin man fetur."

A watan Maris da ta gabata, gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta sanar da cewa kamfanin man fetur na Najeriya ba zai ci gaba da saka wani banbanci tsakanin farashin da aka samu man fetur ba da kuma wanda za a siyar da shi.

A saboda hakan, za a dinga duba farashin man fetur a kowanne wata domin ya zama daidai da yadda danyen man fetur yake a kasuwannin duniya.

"Cire tallafin tuni gwamnatocin da suka shude suka dubeshi a matsayin wata hanya ta kawo ci gaban kasar baki daya.

"Wadannan gyare-gyaren sune suka zama dole. Gwamnatoci sun shude, kuma sun ta yin wannan tunanin, amma sun kasa aiwatar da shi," yace.

Kamar yadda Shehu yace, Buhari ya nuna jajircewa da ba kowa zai iya bayyanawa ba saboda matakin da ya dauka domin ganin walwala da ci gaban kasa.

"A duk lokacin da ake kawo gyara, shugaban kasa yana bukatar goyon baya da fahimtar dukkan 'yan kasa har da 'yan adawa, kungiyoyin kwadago da kungiyoyi masu zaman kansu," hadimin shugaban kasar yace.

"A lokutan kalubale irin wannan, shugaban kasar na kokarin ganin ci gaba ba siyasa ba. Tarihi zai yi masa jinjina nan gaba a maimakon caccakarsa da kalubalen da ake fuskanta daga 'yan adawa," yace.

Dalilin da yasa gwamnatin tarayya ta cire tallafin man fetur - Fadar shugaban kasa
Dalilin da yasa gwamnatin tarayya ta cire tallafin man fetur - Fadar shugaban kasa. Hoto daga The Cable
Asali: UGC

KU KARANTA: Kaduna: 'Yan bindiga sun kai hari Kajuru, mutum 2 sun rasu, an yi awon gaba da 5

Legit.ng ta ruwaito cewa, mutanen Najeriya sun koka da karin kimanin 50% da aka yi a farashin wutar lantarki. Marasa karfi su na ganin babu tausayi a wannan mataki da aka dauka.

Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto a ranar Laraba game da yadda masu aikin hannu, malaman makaranta da ‘yan kasuwa su ke ta faman korafi a kan karin da aka yi.

A bangaren lantarki, an yi karin kudi ta yadda masu samun wuta na akalla sa’a 12 a rana za su ga canjin farashi da kusan 50%, a daidai lokacin da ake kokawa da tattalin arziki.

Wannan sauyi da aka samu a farashin wuta ba zai shafi talaka tubus ba, amma ana ganin mafi yawan mutane za su ga tasirin karin kudin saboda taba ‘yan kasuwa da aka yi.

A daidai wannan lokaci kuma NNPC ta kara farashin litar man fetur daga N138.62 zuwa N147.67. Wannan shi ne farashin da za a rika saidawa manyan dillalai mai a kan sari.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel